Ministar Jinƙai ta jajanta kan faɗowar jirgin saman sojoji

Daga WAKILIN MU

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana alhinin ta kan faɗowar jirgin saman Rundunar Mayaƙan Sama ta Nijeriya (NAF) ƙirar Beechcraft KingAir B350i Aircraft a ranar Lahadi a Abuja.

Rahotanni sun ce jirgin ya samu matsalar inji bayan ya tashi sannan ya faɗo ƙasa.

Hajiya Sadiya ta bayyana baƙin ciki kan haɗarin jirgin da kuma asarar rayukan waɗanda ke cikin jirgin da aka yi.

Ta ce, “Ina cikin tsananin alhini da baƙin cikin wannan abu maras daɗi da ya faru. Ina miƙa gaisuwa ta ga Rundunar Mayaƙan Sama da iyalan waɗanda su ka ran su a faɗowar jirgin.

“Rundunar Mayaƙan Sama ta na bada matuƙar tallafi ga ayyukan mu na kai kayan agaji tun daga farkon kafa wannan Ma’aikata.

“Sun taimaka wajen ɗaukar kayan agaji ga mutanen da wani abu ya faru gare su musamman a lokacin zaman tilas don rage yaɗuwar cutar korona a cikin shekarar 2020 da kuma zuwa ga waɗanda annobar ambaliya da harin ‘yan bindiga da rikice-rikicen jama’a da sauran bala’o’i su ka shafa.

“Mu na godiya kan ayyukan ma’aikatan jiragen su, musamman matuƙan jiragen waɗanda su ka shafe ɗaruruwan awoyi su na tuƙa mu zuwa da dawowa ga yankunan da bala’o’i da sauran al’amuran jinƙai su ka shafa.

“Mu na addu’ar Allah ya bada haƙuri ga iyalan su da su ka bari a baya kuma ya ba su jimirin jure wannan rashi na masoyan su da su ka yi.”

Fasinjoji bakwai ne a cikin jirgin, ciki har da matuƙa biyu.

Hukumar Mayaƙan Sama ta bayyana cewa jirgin ya faɗo ne ranar Lahadi, 21 ga Fabrairu, 2021 a lokacin da ya yi ƙoƙarin dawowa Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja jim kaɗan bayan ya samu matsalar inji a kan hanyar sa ta zuwa Minna.

Hukumar ta ce jirgin ya tashi ne domin ya je ya yi shawagi a saman Jihar Neja da kewaye da nufin ko ma’aikatan za su ga wasu ɗalibai da malaman makaranta da aka sace daga Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara, Jihar Neja.

Mutum bakwai da su ka rasu a haɗarin su ne:

a. Flight Lieutenant Haruna Gadzama (direban jirgin)

b. Flight Lieutenant Henry Piyo (mataimakin direba)

c. Flying Officer Micheal Okpara (Airborne Tactical Observation System (ATOS) Specialist)

d. Warrant Officer Bassey Etim (ATOS Specialist)

e. Flight Sergeant Olasunkanmi Olawunmi (ATOS Specialist)

f. Sergeant Ugochukwu Oluka (ATOS Specialist)

g. Aircraftman Adewale Johnson (Onboard Technician).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *