Ministoci: Sunan mawallafin jaridun Blueprint, Manhaja ya leƙo a sunayen da Tinubu ya miƙa wa Majalisa

Daga BASHIR ISAH

Sunan mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya leƙo a rukunin farko na sunayen da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawan don tabbatar da su a muƙaman ministoci.

Tinubu ya miƙa sunayen ga majalisa ne ta hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Hon Femi Gbajabiamila, a ranar Alhamis.

Sunayen mutum 28 Tinubu ya miƙa wa majalisar da suka haɗa da: Abubakar Momoh, Ambasada Yusuf Maitama, Tukur, Arch. Ahmed Dangiwa, Barr. Hannatu Musawa da Chief Uche Nnaji.

Sai kuma Dr. Berta Edu, Dr. Dorris Aniche Uzoka, Nyesom Wike, Badaru Abubakar, Nasiru Ahmed Elrufai, Rt. Hon. Ekperipe Ekpo, Hon. Nkiru Onyeojiocha, Hon. Olubunmi Tunji Ojo da kuma Hon Stella Okotette.

Sauran su ne, Hon. Uju Kennedy Ohaneye, Mr. Bello Muhammad G., Mr. Dele Alake , Mr. Lateef Fagbemi ( SAN), Mr. Olawale Edun, Mr. Waheed Adebayo Adelabu da Mrs Iman Suleiman Ibrahim.

Haɗa da Fargesa Ali Pate, Fagesa Joseph, Sanata Abubakar Kyari, Sanata John Enoh da kuma Sanata Sani Abubakar Danladi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *