Ministocin wajen Sin da Ukraine sun tattauna ta wayar tarho kan halin da ake ciki a Ukraine

Daga CRI HAUSA

A jiya Talata, mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho bisa buƙatar da ministan harkokin wajen ƙasar Ukraine, Dmytro Kuleba ya yi masa.

Kuleba ya yi wa Wang ƙarin bayani game da zagayen farko na tattaunawar da aka gudanar tsakanin Ukraine da Rasha, inda ya bayyana cewa, kawo ƙarshen yaƙin shi ne babban abin da Ukraine ke bai wa fifiko.

A cewar Kuleba, ƙofar Ukraine a buɗe take domin tattaunawa da nufin warware taƙaddamar dake faruwa, kuma tattaunawar Ukraine da Rasha ta gudana ne bisa gaskiya da kyakkyawar manufa.

Ƙasar Sin ta taka muhimmiyar rawa game da batun dake shafar Ukraine, a cewar Kuleba, inda ya bayyana cewa, ƙasar Ukraine a shirye take ta zurfafa tuntuɓar juna da ɓangaren ƙasar Sin, da kuma neman goyon bayan ƙasar Sin domin ta kasance mai shiga tsakani don cimma nasarar tsagaita buɗe wutar rikicin.

Wang ya bayyana cewa, matsayin ƙasar Sin kan batun dake shafar Ukraine a bayyane yake, kuma a shirye take a koda yaushe, ya ƙara da cewa, ƙasar Sin a ko da yaushe tana tsayawa kan manufar mutunta ikon da dukkan ƙasashe ke da shi da yankunansu.

Game da halin da ake ciki, ƙasar Sin ta buƙaci ɓangarorin Ukraine da Rasha da su lalibo bakin zaren warware rikicin ta hanyar tattaunawar sulhu, kana su amince da dukkan muhimman ƙoƙarin da ƙasa da ƙasa ke yi na neman warware rikicin ta hanyar matakan siyasa, in ji Wang.

Fassarawa: Ahmad Fagam