Misalin da Sheikh Ahmad Gumi ya kafa

Tare da IBRAHIM SHEME

Ba kasafai Sheikh Dakta Ahmad Gumi ya kan nasa kwan sa ba tare da zakara ba; manufa, ba ya magana ko aikata wani abu ba tare da kwakkwarar hujja ba. Sau da yawa, kalaman sa ba su yi wasu dadi saboda an saba da son jin magana mai dadi, musamman wajen voye gaskiya tare da zama a kan akasin ta.

Dakta Gumi ya sha yin suka kan halin rashin tsaro da ake ciki a kasar nan, musamman a Arewa. Kuma ya sha yin nuni da hanyar da ya kamata a bi domin a bulle zuwa inda za a samu sa’ida. Wayyo, ba kowa ya kula ba; wadanda su ka kula din ma ba su dauki abin da gasken gaske ba.

Amma kuma ba shi kadai ba ne malamin da ya ke yin magana kan halin da Arewa ta ke ciki; malaman addini da dama ’yan’uwan sa sun sha yin magana, wasu ma har da yin dakuwa ta cikin riga! Shin me ya kamaci mumini ya yi idan al’amari ya rincabe? Hadisi ya ce to ya fito ya yi jihadi a kai: na daya, ya kauda abin da hannun sa; idan hakan ta ki, to ya soki lamirin abin a bayyane da bakin sa; idan hakan ba za ta yiwu ba, to ya ki abin a cikin ran sa.
Malamai, masana, sun sha sukar lamirin halin da mu ke ciki. Amma yawanci a nan su ka tsaya da jihadin su. Sun bar aikin kaudawar a hannun hukumomin da aka kafa domin yin hakan, irin su ‘yan sanda da sojoji. Amma Sheikh Gumi fa? Da alama nasa jihadin bai tsaya a nan ba. Shi Malam fitowa ya yi ya na kokarin kauda wannan abin kin da hannun sa. Mun ji an ce hakan ya faru ne bayan ya lura da cewa yakar abin da fatar baki kadai ba zai wadatar ba, sai an motsa kafa.

A karo uku, malamin ya tashi ya bar zauren sa, ya shiga daji har inda tushen matsalar ta ke, ya gana da barayin da gwamnati ta gaza ganin bayan su. Na farko, ya je dajin Jere can a hanyar Kaduna zuwa Abuja, ya yi tozali da Fulani masu tare hanya su na satar mutane domin a biya su diyya ko su kashe mutum. Na biyu, ya kutsa cikin dajin Giwa inda a can ma ya tattauna da irin wadannan batagarin, har ma da iyayen su da matan su da ’ya’yan su manya da kanana. Na uku, ya je dajin Kagarko ya yi irin wannan ganawar da Fulani.

A lokacin wadannan tafiye-tafiye, Sheikh tare da ‘yan rakiyar sa, wadanda su ka hada da manya da kananan jami’an tsaro da kuma malamai, sun ji daga bakin da ba ya karya kan dalilin ta’asar da ke aukuwa – wato su Fulanin. Yanzu babu sauran sirri ko nuku-nuku, kowa ya san dalilin da ya sa wadannan bayin Allah su ka hana kowa barci da idanun sa rufe tare da minshari.

Maganar daya ce: an zalunci Fulani. Ana kama su ana wulakanta su. Ana karbe masu shanu. Ana harbe wasun su. Kuma duk a kan dalilin da bai taka kara ya karya ba. Idan ana son lumana, to a daina.

Da gaske ne akwai ’yan iskan Fulani a daji kamar yadda akwai ’yan iskan Hausawa a cikin gari. Tun tuni kwaya ta shiga rugage, tare da nau’o’in rayuwar zamani da su ka antayo daga Turai da Amurka zuwa kowane sako na duniya; wasu matasan Fulanin sun daina girmama dattijan su. Su yanzu cin gashin kan su su ke yi. Da yawa sun lalace, ba su ganin kan kowa da gashi. Wasun su sun zama barayi, su na tare hanya tunda sun lasa sun ji zaki.

Tilas ne a kama Bafillacen da ya yi laifi domin a hukunta shi. To amma wane irin hukuncin? Idan Bafillace ya yi laifi, ana yi masa hukuncin da ya saba wa kundin finalkod. Jami’an tsaro kan rike shi su azabtar da shi har sai imanin sa ya rabu da shi kamar yadda su ma ba su saka imani a cikin hukuncin su. Sau da yawa sai uban sa ya saida shanu da dama ya kai kudin kafin a sako shi. Ta wannan hanyar an talauta Fulani da dama.

To, ga kuma sauyin yanayin ita kan ta duniyar. Yanzu kiwo bai ci sosai kamar da. Sai da juriya. Abincin dabbobi ya yi wuya. Talaucin da ke damun duniya ma ya kutsa kai cikin rugage, ya sauya wa Fulani rayuwa. Sannan fadadar birane ta na ture Fulani daga matsugunin su don su ba Hausawa da sauran yaruka wurin zama. Ga kuma yanka gonaki da ‘yan boko ke ta yi, su na cinye labuka inda shanu za su yi kiwo ko su bi su wuce. Dadadden lamari ne, amma an bar shi ya azance.

Wani abin da ya kazance kuma shi ne mu’amalar Fulani da wasu kabilun. A da, Bafillace bai da matsala da kowa a Kudancin Kaduna, Inugu ko Ibadan. Ana zaman ‘ba ni gishiri in ba ka manda’. Amma a yau rikice-rikice sun bata mu’amala tsakanin makiyaya da wasu al’ummomin Nijeriya. Yau har ta kai gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya bada oda a ranar Litinin da ta gabata wai ya ba Fulani makiyaya kwana bakwai su fice daga jihar sa, sai ka ce jihar tasa wata kasa ce mai cin gashin kan ta, ba wani yanki na Nijeriya ba. Da alama, gwamnan bai san cewa su ma Fulani ‘yan Nijeriya ba ne. Akwai ma irin wannan tunanin nasa game da Fulani a Binuwai da Filato da Kudancin Kaduna.

Duk laifin gwamnati ne fa. Da alama, a tsawon lokaci Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi ba su dauki Fulani a bakin komai ba. Shi ya sa su ka bar al’amarin ya tabarbare. Sun sa ido lokacin da lalacewar ta fara da kadan da kadan har ta kai intaha, sha’anin ya kwace. Ba su yi irin tsawatawar da ya kamata su rika yi ba.

Halin ko-in-kula na gwamnatoci ya sa duk wani tsarin cigaba, ba a saka Fulani a ciki. E, na ji an yi wa makiyaya shirin ilmantar da ’ya’yan su, to daga nan fa? Shirin ma ya ci wata nasara ta a zo a gani kuwa? Fulani nawa ne za a nuna a matsayin wadanda su ka ci moriyar sa har su ka zama wani abu a kasar nan?

Saken da gwamnati ta yi kan lamarin Fulani ya vaci. Qungiyoyin kare hakkin Fulanin kuma duk sun zama na siyasa da kasuwanci; sun koma ‘yan amshin shatan masu mulki. Hakan ya sa an ture Fulani gefe a cikin kokowar samun ababen more rayuwa. Fulani na rayuwa a jihar Kaduna a yau kamar yadda kakannin kakannin kakannin su su ka yi a zamanin Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo. ’Yan bokon Arewa da ke cikin gari ba su damu da rayuwar makiyaya da ke daji ba. Ga shi kuma da yawan su ma tushen su Fulanin ne; duba ka gani daga kan shugaban kasa har zuwa kan gwamnoni da ministoci da ‘yan majalisa da sarakuna da manyan ma’aikata da manyan ‘yan kasuwa. Yanzu su ne wadanda maharan da ke tare hanya su ke kamawa don a biya su kudin fansa.

Sheikh Gumi ya hango duk wannan.Ya ga cewa nade hannu ba shi ne mafita ba.Tilas mu sake rungumar ‘yan’uwan mu Fulani domin wallahi babu yadda za mu yi mu rayu ba tare da su ba. Kasar nan ba tamu ce mu kadai ba. Su ma tasu ce. Idan mun nuna halin ko-in-kula gare su, to duk abin da ya faru gare mu laifin mu ne. Ciki har da garkuwa da ake yi da mu.

Tilas a yaba wa Dakta Gumi da ya nuna kyakkyawan misali. Allah ya sa gwamnati ta ba shi cikakken hadin kai domin a samu wanzar da zaman lafiya da Fulani da ma duk wanda ke voyewa a bukkar Fulani ya na aikata ta’asa. Kada gwamnati ta yi kumbiya-kumbiya da wannan hobbasan da Malam ke yi. Mun san cewa ba domin neman kudi ko muqami ko wata alfarma ya ke yin wannan kokari ba, domin kowa ya san wadannan ba su gaban shi. Ya na yi ne domin taimakon al’ummar kasa baki daya. Su ma ‘yan tawagar sa, wadanda su ke saida ran su don ganin wannan buri ya cika, Allah ya saka masu da alheri.

Ina kira ga sauran malamai da cewa kada jihadin su ya tsaya a kan mumbari kadai. Arewa ta yi tabarbarewar da lallai sai an motsa kafa. An motsa baki kam, Allah ya saka da alheri, to lokaci ya yi da ya kamata a fita a shiga mota a kama hanya a ga duk wanda ya kamata a gani don kawo karshen halin ha’ula’in da ake ciki. Malamai su tuna, addini ba ya yiwuwa a cikin yanayin rashin tsaro da fargaba. Idan an samu kwanciyar hankali, an taimaki addinin ne. Allah ya ganar da mu baki daya.