Miyetti Allah ta sanar da ɓacewar Mataimakin Shugaba na Ƙasa, Lamiɗo

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya (MACBAN), ta sanar da ɓacewar Mataimakin Shugabanta na Ƙasa, Engr. Munnir Atiku Lamido.

Mai magana da yawun ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Muhammad Nura Abdullahi, shi ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce, “muna sanar da al’umma da ma hukumomin tsaro cewa, Engr. Munnir Atiku Lamiɗo ya ɓace.

“Engr. Munnir shi ne Mataimakin Shugaban MACBAN na Ƙasa.

“Ya bar gidansa da ke Katsina a ranar Juma’a, 23 ga Yuni, 2023, da nufin zuwa Kaduna, kuma har zuwa yanzu ba a san inda yake ba,” in ji shi.

Sanarwar ta nuna cewa, a ranar Alhamis aka gano motar Lamiɗo a hanyar tsakanin Jos da Kaduna kusa da garin Mararraban Jos ajiye a gefen hanya da woyoyinsa duk a ciki.

Kawo yanzu ƙoƙarin da aka yi domin gano shi ya ci tura, in ji sanarwar.

MACBAN ta ce duk wanda ke da muhimman bayanai da za su taimaka a gano inda Lamiɗo yake, ya tuntuɓi ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ofishin ƙungiyar a kowane sashen ƙasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *