Miyetti Allah za ta iya kawo ƙarshen hare-haren ’yan bindiga – Sarkin Musulmi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah (MACBAN), na iya ba da gudunmawa wajen magance matsalar hare-haren ’yan bindiga a ƙasar nan.

Sarkin Musulmi, ya ce shugabancin MACBAN na iya taimaka wa wajen kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga da ke garkuwa da mutane a Nijeriya.

Ya bayyana haka ne a lokacin rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar MACBAN a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

A cewar sarkin, “kowa ya san Fulani suna tashi daga wani waje zuwa wani. Suna zuwa ko’ina suna yin aure. Kuma mu masu son zaman lafiya ne.

“Amma ta yaya muka kai ga halin da muke ciki a yanzu, mun gano ’ya’yanmu Fulani ne, amma ba dukkaninsu ne suka shiga harkar fashi da garkuwa da mutane ba.

“Idan muka gana da shugabannin wannan ƙungiya za su tattauna yadda za a shawo kan lamarin, domin lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen matsalar nan.

“Sama da shekara 48 da kafuwar MACBAN, muna buƙatar samun wasu sabbin abubuwa da sabbin dabaru a cikin kundin tsarin mulkinta.”

A baya-bayan nan dai ana alaƙanta Fulani makiyaya da yin garkuwa da mutane da aikata fashin daji a ƙasar nan.

Ana zargin Fulani makiyaya da kai hare-hare kan manoma tare da korar al’umma, da kuma kai hare-hare kan cibiyoyin addini a faɗin ƙasar nan.

Ana kuma alaƙanta makiyaya masu ɗauke da makamai sun karɓi biliyoyin kuɗi a matsayin kuɗin fansa daga iyalan mutanen da ake zargin suna sacewa.