MOFA: Sin da Amurka na iya yin hulɗar abota na bai ɗaya

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai Jumma’ar nan cewa, a matsayinsu na ƙasashen dake yankin Asiya da tekun Pasifik, ƙasashen Sin da Amurka za su iya yin hulɗar abokantaka na bai ɗaya.

Zhao ya bayyana haka ne a lokacin da yake ƙarin haske, kan wani taro na musamman da ya gudana tsakanin Amurka da kuma ƙungiyar ƙasashen da ke yankin kudu maso gabashin Asiya (ASEAN), a birnin Washington a ranakun Alhamis da Jumma’a, don tunawa da cikin shekaru 45 da ƙulla hulɗar haɗin gwiwa tsakanin ɓangarorin biyu.

A yayin taron, Amurka ta sanar da wani ƙunshin shirin raya ƙasa ga ƙungiyar ta ASEAN na sama da dalar Amurka miliyan 150, wanda ya shafi samar da ababen more rayuwa, da tsaro da yaƙi da cutar COVID-19.

Da yake bayani kan raya dangantaka tsakanin ƙasashen yankin Asiya da tekun Pasifik, Zhao ya ce muhimmin abu shi ne, a saurari buƙatarsu ta kiyaye zaman lafiya, da zurfafa haɗin gwiwa da neman samun ci gaba tare.

Ƙasar Sin da ƙungiyar ASEAN, ba sa yin abubuwa marasa amfani, ko kuma sa ƙaimi ga yin fito na fito da juna a tsakanin rukunoni.

Yana mai cewa, ƙasar Sin tana maraba da duk wani shiri na haɗin gwiwa da zai taimaka ga samun dauwamammen cigaba mai ɗorewa da wadata tare a yankin.

Fassarawa: Ibrahim