MOPPAN ta gurfanar da wanda ya yi wa matan Kannywood ɓatanci

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar masu shirya finafinai ta MOPPAN, ta gurfanar da wani mai suna Sufin Zamani a gaban hukumar DSS saboda ɓatancin da ya yi wa matan Kannywood.

MOPPAN ta ce ta ɗauki wannan mataki ne biyo bayan ƙorafin da wasu matan Kannywood suka aikewa shugabanta na ƙasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, mai taken: “Ƙorafin cin zarafi da wani mawaƙi mai suna ‘Sufin Zamani,” takardar da tsohuwar jarumar fim Wasila Isma’il ta sanya wa hannu, a madadin Matan Kannywood.

Wannan ya sanya MOPPAN gaggauta shiga binciken ƙorafin, inda daga bisani ta rubuta wa Hukumar DSS, domin yin abin da ya dace.

Sanarwar manema labarai da MOPPAN ta fitar ta hannun Kakakinta na Ƙasa, Al-Amin Ciroma ta nuna cewa, bayan da MOPPAN ta tuntuɓi DSS ne, daga nan ita kuma DSS ɗin ta gudanar da bincikenta inda ta nemo gami da cafke mawaƙin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, a ranar Laraba, 22 ga Yuni, DSS ta damƙe Sufin Zamani, kana ta bayar da belinsa a ranar Alhamis da ta gabata, a bisa sharuɗɗan da suka haɗa da: Yin bidiyo da ‘audio’ na ban-haƙuri da kuma ƙaryata kansa game da waƙar ɓatancin da ya yi; yin waƙa kishiyar wacce ya yi, wato ya yabi matan Kannywood da faɗin alherinsu kuma ya nuna masu zaman aure ne.

Sauran sharuɗɗan su ne, rubuta wa MOPPAN takardar ban-haƙuri; rubuta wa hukuma takardar alƙawari kan cewar ba zai kuma yin ɓatanci ga duk wani ɗan fim ba, sannan bayan haka hukumar DSS za ta yi masa hukunci da ya dace saboda ƙaryar da hukumar ta ce ya yi mata a farkon kamun da aka yi masa.

Duka waɗannan na zuwa ne bayan da Sufin Zamanin ya yi iƙirarin aikata laifin da aka tuhume shi da aikatawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *