MOPPAN ta shirya taron wayar da kai kan amfanin soshiyal midiya

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwararru ta Masu Shirya Finafinan Hausa ta Nijeriya, wato Motion Picture Practitioners Associations of Nigeria, tare da haɗin gwiwar Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, sun shirya taron wayar da kan masu sana’ar ta shirin fim a kan yin amfani da soshiyal midiya ga ’yan Masana’antar Kannywwod.

Taron na wuni guda, wanda aka gudanar da shi a ranar Alhamis, 10 ga Maris, 2022, a ɗakin taro na Kannywwod TV da ke titin Muhammadu Buhari a Birnin Kano, ya samu halartar masu gudanar da harkar fim da suke dukkan jihohi na Arewacin Nijeriya da ma wasu jihohin Kudu.

Tun da farko, da ya ke gabatar da jawabi a game da manufar taron, Shugaban Ƙungiyar MOPPAN na Ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya bayyana taron a matsayin wani ɓangare na aikin da ƙungiyar ta sa a gaba na wayar da kan masu harkar fim da kuma ilimintar da su a kan harkokin kasuwancin na fim, don haka idan mutum ya samu ilimi to sai ya je ya yi abin da ya kamata ya yi.

Shi ma da yake jawabi a wajen, babban baƙo mai jawabi, Dakta Nura Ibrahim, wanda Rukayya Yusuf ta wakilce shi, ta bayyana cewar, “Hanyoyin sadarwa na zamani wanda a ke kira soshiyal midiya a yanzu ya kawo cigaba ta ɓangaren kasuwanci da harkokin rayuwar yau da kullum.”

Ta ƙara da cewar, “harkokin labarai da na fim a yanzu duk sun koma soshiyal midiya wanda a nan a ke cin kasuwar labarai da kuma fim, to amma dai a wannan lokacin ya zama wajibi a san yadda za a yi amfani da shi, don haka ‘yan jarida da kuma harkar fim a yanzu a soshiyal midiya a ke samun labari da dumi-dumin su, sai an yi amfani da soshiyal midiya a yanzu wajen isar da saqo cikin sauri, mutum ko a Ina yake a duniya za ka iya yin magana da shi saboda damar da mu ka samu.

A yanzu fiye da rabin mutanen duniya suna amfani da soshiyal midiya, kuma a nan Nijeriya mutane sama da miliyan 90 suna amfani da soshiyal midiya, zai yi kyau mu fara tunanin yadda za mu fara amfani da ita domin harka ce da idan mutum yana amfani da ita a wajen saƙon da kake sakawa za a san yadda halayyarka take ba sai an tambaya ba.

Kada mutum ya yi amfani da damar sa a soshiyal midiya don aikin da ba zai amfanar da shi ba, kada mu yaɗa abin da ba na gaskiya ba ne, domin idan kana ba da labarin da ba na gaskiya ba, ko na shirme, mutane ba za su rinƙa bibiyar ka ba, don sun san ba gaskiya ba ne, sai su guje ka.

Ya kamata ku kula da abin da mutane za su amfana a gare ka ta yadda kullum za su rinqa bibiyar ka.”

Daga ƙarshe Malam Khalid Musa, ya yi sharhi a kan jawabin na ta, in da ya yi kira ga masu harkar fim su yi amfani da jawabin da aka gabatar, domin gyara kasuwancinsu, kuma kada su yi amfani da soshiyal midiya wajen yaɗa ƙabilanci ko cusa gaba a cikin jama’a.

Da dama daga cikin mahalarta taron sun nuna gamsuwar su da jawabin da aka yi mu su, kuma za su tafi da ƙoƙarin yin amfani da abin da suka koya.