MOPPAN ta taya Afakallah murna kan sabon naɗin da aka yi masa

Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), ƙarƙashin jagorancin Alhaji Habibu Barde, ta miƙa saƙon taya murna da fatan alheri ga Alhaji Ismail Mohammed Na’Abba da aka fi sani da Afakallah.

MOPPAN ta taya Afakallah murna ne bisa naɗin da aka yi masa na zama ɗaya daga cikin mambobin Hukumar Gudanarwa na Jami’ar Fasaha ta Jihar Jigawa.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 19/5/2024 da kuma sa hannun sakatarenta na ƙassa, Al-Amin Ciroma.

Ƙungiyar ta ce Afakallah na ɗaya daga cikin zaƙaƙuran mutanen da suka bunƙasa masa’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood. Don haka ta ce ba ta yi mamakin naɗin da aka yi masa ba saboda cancantarsa.

Ta ƙara da cewa, a lokacin da yake riƙe da muƙamin Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Afakallah ya yi aiki tuƙuru wajen inganta masana’antar Kannywood.

Sanarwar ta ce, ƙungiyar na da yaƙinin sabon naɗin nasa zai ba shi damar ci gaba da yi wa al’umma hidima musamman Jami’ar Fasaha ta Jihar Jigawa.