MOPPAN ta yi haɗin gwiwa da NDLEA don yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirin Fim (MOPPAN) ta bayyana cewar ta samu damar haɗin gwiwa da hukumar Hukumar Yaƙi da Sha da Kuma Yaƙi da Fataucin Miyagu Ƙwayoyi (NDLEA) domin bayar da tata gudunmawa wajen yaƙi da shan ƙwayoyi.

Cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun jami’inta na hulɗa da jama’a na ƙasa, Al-Amin Ciroma, MOPPAN ta ce ta cimma wannan nasara ne sakamakon takardar da ta rubuta wa hukumar ta neman yin haɗin gwiwa wajen cigaba da yaƙi da miyagun ƙwayoyi a faɗin Nijeriya.

Sanarwar ta nuna biyo bayan wannan haɗakar, Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, na sanar da masana’antar Kannywood, cewa Shugaban hukumar na ƙasa, wato Brig. Gen. Muhammad Buba Marwa (rtd), zai kawo wa ƙungiyar MOPPAN /Kannywood ziyara ta musamman.

MOPPAN za ta karɓi baƙuncin shugaban da tawagarsa ne a babban ɗakin taro na Kannywood TV da ke Kano a ranar Laraba 1 ga Satumban 2021, da misalin ƙarfe 1:30 na rana.

Bisa wannan dalili ne MOPPAN ta ce tana gayyatar dukkannin masu ruwa da tsaki a wannan masana’anta da su halarci wannan taro mai muhimmanci.

A cewar sanarwar, “Taron zai samar da sahihiyar hanyar samar da kyakkyawar hanyar gudanar da ingantaccen tsari tsakanin hukumar da MOPPAN.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *