MOPPAN ta yi ta’aziyyar rasuwar Baba Karƙuzu

Ƙungiyar MOPPAN ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan fitaccen jarumi, Abdullahi Shu’aibu, wanda aka fi sani da Baba Ƙarƙuzu, bayan rasuwarsa a ranar 25 ga Maris, 2025.

A cikin wata sanarwa da shugaban MOPPAN, Mallam Maikudi Umar (Cashman) ya fitar, ya bayyana rasuwar Baba Ƙarƙuzu a matsayin babban rashi ga masana’antar Kannywood da ɗaukacin al’ummar Arewacin Najeriya.

Sanarwar ta ce, “Rasuwar wannan babban jarumi, uba, kuma ɗaya daga cikin ginshiƙan da suka aza harsashin wannan masana’anta, babbar rashi ce. Muna addu’a Allah ya gafarta masa, ya sanya shi cikin rahamarsa, sannan ya bai wa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.”

Shugaban ya jaddada cewa Baba Ƙarƙuzu ya taka rawar gani wajen ci gaban Kannywood, kuma girmamawa gare shi ba za ta gushe ba a zukatan masoya da abokan aikinsa.