Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kocin Roma, Jose Mourinho ya musanta yunƙurin tunzura shugabannin ƙungiyar da wani hoto a shafinsa na Instagram amma ya ce abubuwa ba su daidaita ba.
A hoton ana iya ganin Mourinho mai shekaru 60 da ma’aikatansa suna rungumar wani abin da ba a gani bayan Roma ta gaza ɗauko sabon ɗan wasan da zai maye gurbin Tammy Abraham wanda ke ɗauke da rauni.
An saka hoton ne a ƙarshen atisayen da ƙungiyar Roma ta yi a ƙasar Portugal mako ɗaya da ya wuce.
An ɗauke ɗan wasan gaban Ingila Abraham, mai shekara 25, jim kaɗan bayan fara wasan qarshe na Seria A da ƙungiyar ta yi da Spezia a watan Yuni kuma ba a sa ran zai sake buga wasa kafin ƙarshen shekarar nan.
Ana alaƙanta Roma da dan wasan gaba na ƙasar Sipaniya Alvaro Morata da ɗan wasan gaba na Atalanta Gianluca Scamacca amma ba a cimma nasara da cinikin kowannensu ba.
Morata ya cigaba da zama a Atletico Madrid, yayin da Scamacca ke daf da komawa Atalanta daga West Ham.