Kamfanin sadarwa na MTN ya ce yana shirin ƙara kuɗin kira da farashin Data saboda tsadar rayuwa da yawan harajin da aka ɗora wa kamfanin.
Bayanin haka na ƙunshe ne cikin rahoton zangon farko na da kamfanin ya fitar kwanan nan.
Kamfanin ya ce da alama yanayin kasuwanci a ragowar 2023 zai kasance mai tattare da ƙalubale.
Don haka kamfanin ya ce shi ma zai duba sannan ya yi abin da ya dace don iya tafiyar da harkokinsa a wannan lokaci na ƙalubale.
Kamfanin ya ƙara da cewa, ƙarin farashin shi ne mafita a wannan hali, saboda ta haka ne zai iya samun kuɗin shiga a wadace don ci gaba da tattalin ayyukansa yadda ya kamata.
“Za mu ci gaba da tattaunawa da hukumomin da suka dace kan buƙatar yin ƙarin farashin,” Kamar yadda babban jami’in kamfanin na MTN, Ralph Mupita, ya bayyana a sanarwar da ya fitar.
Tuni dai masu amfani da layikan sadarwa na MTN suka koka kan tsadar data da suke fuskanta daga kamfanin.
Wasu kwastomin kamfanin na kallon ƙarin farashin da kamfanin ke shirin yi a matsayin karɓe wa jama’a kuɗaɗe, saboda a ra’ayinsu kamfanin ya samu ribar miliyoyin da bai kamata yana yi wa kwastominsa ƙarin farashi ba.