Mu haɗa kai don cigaban Nijeriya – Ministan Labarai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan Yaɗa Labaran Nijeriya, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai su inganta al’amuran ƙasar.

A wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar yaɗa labarai ta tarayya, Malam Suleiman Haruna, ya fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa ministan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) ta kai masa, inda ministan ya bayyana cewa, aikin sa daga shugaban ƙasa Bola Tinubu shi ne ba da fifiko da sake fasalin qasa don inganta zaman lafiya, haɗin kai, cigaban al’umma.

“Wannan ita ce ƙasarmu; Dole ne dukkanmu mu haɗu mu kasance masu gaskiya da riƙon amana ga kawukanmu, kuma mu tabbatar da cewa duk abin da ke damunmu an gyara shi,” inji shi.

Idris ya buqaci mambobin cibiyar da su haɗa kai da shi wajen gudanar da wannan aiki, inda ya jaddada muhimmancin gaskiya da riƙon amana wajen gyara duk wata matsala da ka iya kawo cikas ga cigaban ƙasa.

Ya fahimci muhimmiyar rawar da NIPR ta taka wajen samar da kyakykyawan ƙima ga Nijeriya, sannan ya ƙara musu ƙwarin gwiwar cigaba da ƙoƙarinsu tare da sauran mambobin wannan fanni.

“Dukkanmu mun san cewa NIPR ta taka muhimmiyar rawa a tsawon shekaru wajen samar da kyakkyawan fuska ga ƙasarmu. Muna buƙatar ƙara zurfafa ƙoƙarin tare da sauran membobin wannan fanni,” inji shi.

A nasa jawabin, shugaban NIPR na ƙasa, Malam Mukhtar Zubairu Sirajo, ya bayyana jin daɗinsa da naɗin da aka yi wa Alhaji Idris a matsayin minista, ya kuma bayyana shi a matsayin ƙwararre.

Ya buƙaci ministan da ya samar da hanyoyin sadarwa tsakanin gwamnati da jama’a tare da bayar da goyon bayan NIPR domin cimma burin sa.

“A matsayinmu na memba na cibiyar, mun yi imanin za ku yi amfani da ladabinku na gaskiya da basirarku a matsayin abin hulɗa da jama’a don canja ƙasar.”