Mu kawar da bara, domin bara ba addini ba ce

Daga MUHAMMAD BALA GARBA a Maiduguri 
                       
A duk lokacin da aka ambaci kawar da Bara, sai wasu su ɗauki hakan a matsayin wani yunƙuri na hana karatun allo ko kuma Alƙur’ani mai girma. Wasu rashin sanin ma’anar Baran ne ya sa suke ɗauka karatun allo ake son hanawa. Wasu kuma suna sane da abin da ake nufi, amma saboda wasu ɓoyayyun manufofinsu da ke ƙarƙashin ƙasa ya sa suke sauya ma’anar maganar zuwa hana karatun allo ko kuma Alƙur’ani mai girma. 

Da farko dai yana da kyau mu san cewa, kalmar ‘Bara’ tana da ma’anoni guda biyu: Ma’ana ta farko, tana nufin yaron gida. Ma’ana ta biyu kuma tana nufin neman sadaka kamar yadda wasu suka ɗauki kalmar ‘almajiri’ (mai yin Bara). Sai dai ba dole ba ne mabaraci ya kasance slmajiri, domin akwai Almajiran da ba sa yin bara. Idan kuwa haka ne, yana da kyau mu san wane ne almajiri? Sannan kuma mecece bara? 

Asalin kalmar almajiri?
Kalmar Almajiri ta samo asali ne daga harshen Larabci ‘Almuhajir’, wato wanda ya yi kaura daga wani muhalli zuwa wani. Daga baya kalmar ta rikiɗe ta koma almajiri.

Wane ne Almajiri?
Almajiri yana nufin ɗalibi ko kuma mai neman ilimi. Dukkanin wanda ke neman ilimi ko da kuwa ilimin addini ne ko na zamani ko na gargajiya ko na koyon aikace-aikace, to wannan sunansa Almajiri. Sai dai kuma akasarin Hausawa a yau na yi wa kalmar Almajiri fassarar mabaraci. Kamar yadda ake danganta yaran da ke barin garuruwansu zuwa wadda ba nasu ba neman ilimin Al-ƙur’ani.

Mecece bara?
Bara wata ɗabi’a ce mai tsohon tarihi a ƙasar Hausa, wadda ba lallai ba ne wani ya bugi ƙirji ya ce san lokacin da aka fara yin ta. Sai dai masana suna ganin ana iya kallon bara ta fuska biyu: wato kafin zuwan Musulunci da kuma bayan zuwan Musulunci. 

Kafin zuwan Musulunci, Hausawa suna kan Maguzanci, kuma tun a wancan lokacin an san su da kyauta da taimakon junansu, don haka ne tun a lokacin akwai al’adar Bara, sai dai an ɗauke ta ne kawai a matsayin taimako da kyautata wa naƙasassu.

Da zuwan Addinin Musulunci sai ya zo da tsarin karatun addini, irin wannan yanayi ne sai ake samun Malaman da suke tattara yara da sunan koyar da su ilimin addini. Sukan bi gari-gari da waɗannan yaran domin a cewar su, karatu ba ya samuwa sai an sha wahala. Bayan sun samu masauki, sai ya zamto ba su da kayan biyan buƙatu, don haka, dole su fita su nemi taimako. Daga haka ne suka mayar da wannan halayya tamkar

sana’ar yi, har ta kai ga zuciyar wasu ta mutu gabaɗaya.

A lokacin Bara ba ta zama abar ƙyama ba, musamman a ƙasar Hausa. Domin a lokacin (kafin zuwan Turawa), wajen ƙarni na goma sha biyu, muna iya kallon bara a wani janibi na dabam. Alal misali, lokacin muna da Sarakuna masu mulki na haƙiƙa da Malamai waɗanda suke karantarwa yadda ya kamata, gami da kula da ‘ya’ya cikin mutunci da kamala.

Sannan a waccan lokacin ba mu da yawaitar jama’a kamar na yau, kuma mutanen waccan lokacin suna da karamci da tausayin wanda bai da shi. Domin za ka ga mabaratan wancan lokacin ba da son ransu suke yin barar ba. Sannan da sun samu abin da suke buƙata, sukan koma muhallinsu. Wannan ya sa wasu mutane idan suka yi noma a ƙarshen shekara, sukan ware wani kaso su kai wa waɗanda suke ganin ba su da ƙarfin da za su iya nomawa, kamar kutare da guragu da makafi. Wannan ya sa wasu daga cikin nakasassun suka daina fita waje yin bara domin sun samu abin da zai wadatar da su.

Almajiranci da bara a yau
Bara a yau ta rikiɗa ta zama roƙo, ana iya kiranta wata gagarumar matsala wadda take kawo koma baya a ƙasar Hausawa. Alal misali, barar ƙananan yara. Iyaye sukan ɗauki ‘ya’yansu su kai su wurin malamai waɗanda suke ba da karatu a matsayin almajirai (masu neman ilimi), wanda daga nan kuma, sai su manta da rayuwar ‘ya’yan. Ba su san cin su ba, ba su san shan su ba, ballatana suturunsu; domin su ma talakawa ne abin da za su ci wuya yake masu. Wasu ma da gangan suke kai ‘ya’yan almajiranci, saboda inda suke kwana ya yi musu kaɗan, kuma ga abincin da uba yake kawowa ba ya isar su, ga shi an hayayyafa da yawa. Don haka, sai ka ga uba ya ɗauki ‘ya’yansa ya kai su can wata uwa duniya mai nisa da sunan karatu ya kai su. 

Wasu iyayen sukan ce ka da a bar yaro ya taho ganin gida har sai ya sauke Alƙur’ani mai girma. Su kuma daga nan sai su kai wajen shekara guda ba su sake waiwayar ‘ya’yan ba. Daga nan sai su ƙulle ɗan abin da bai taka kara ya karya ba su aika wa malamin da ‘ya’yansu suke wajensa a madadin ladan kula da yaran da yake yi.

Da ma shi ma malam yana fama da kansa, ga shi kuma babu wata ƙwaƙƙwarar sana’a da ya dogara da ita, ga shi an tara masa yara a wurinsa, kuma iyayensu sun yi nisa da su. Sai ka ga ba shi da lokacin tarbiyyantar da su, sannan kuma bai damu da halin da yaran za su shiga ba. Yawaicin irin kuɗaɗen da ake aikowa, malaman ne kan sanya su a cikin aljihunsu, kuma ba su fiya damuwa da irin rayuwar da yaran kan kasance a ciki ba.

A halin da ake ciki a yau, irin waɗannan yara da ake kawowa Almajiranci, za ka ringa ganinsu wajen ‘yan tuwo-tuwo da wurin ‘yan Daudu gami da yin sana’ar gwan-gwan; daga nan sai ka ga sun shiga shaye-shayen ƙananan kayan maye irin su; Sigari da Sholisho da Madarar Sukudayin. Domin guraren da suke ziyarta gurare ne na matattarar masu irin waɗannan ɗabi’u. Idan ba a yi sa’a ba kuma, sai yaro ya shiga ta’addaci, shikenan al’umma ta shiga uku. 

Wasu yaran daga nan sai su ɓalle daga makarantar su daina zuwa, su koma can tasha da matattarar ‘yan bola-bola su ci gaba da zama.

Lokaci-lokaci sukan ɓullo makarantar su baiwa Malaman nasu ɗan abin vatarwa na wasu ‘yan kuɗade ko kaya. Su kuma Malaman kan karva gami da yi musu wasu ‘yan nasihohin da ba zai amfane su ba. Idan muka kalli samuwar wannan matsala za mu ga bara ce ta haifar da ita, domin da yaran ba su je ba, da ba za su samu damar zuwa irin wuraren da ya yi sanadiyar gurɓacewarsu ba.

A cikin littafina mai suna ‘GOBARA DAGA KOGI’ (wanda na rubuta akan ƙungiyar Boko Haram) a shafi na casa’in (90), na yi bayani akan mafiya yawan ‘ya’yan ƙungiyar Boko Haram Almajirai ne masu kishin addinin Musuluci amma kuma ba su da ilimin addinin. Yayin da wasun su kuma suna da haddar Alƙur’anin amma kuma ba su da ilimin fassarar shi. Wannan ya sa Mohammad Yusuf ya samu damar yaudarar irin waɗannan yaran wajen cusa musu aƙidunsa na ta’addaci.

Irin illar da waɗannan yaran ke haifarwa tana da yawa sosai, domin ba su samu cikakken ilimin da ake so ba. Ga shi kuma ba su samu kyakkyawar tarbiyya ba. Kun ga kuwa, sun yi biyu babu domin babu cikakken ilimin addini, babu na zamani, sai ka ga yaro ya tashi cikin rashin tausayi. Haka kuma yawanci irin waɗannan yaran ba su fiya komawa garuruwansu ba. Kun ga kenan, an ɓata goma ɗaya ba ta gyaru ba.

Idan muka dawo ɓangaren manya kuma, za mu ga yadda a yau suka mai da Bara sana’a, kai har ta kai ma da wanda ya nakasa da wanda bai nakasa ba duk barar suke. Manyan illolin da bara ta haifar mana a Arewanci Najeriya sun haɗa da:

Lalacewar tarbiyya: – Wanda ke kaiwa ga sace- sace da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da zinace-zinace.

Kangarewa: – Wanda ke sanya rashin tausayin iyaye da ma sauran al’umma baki ɗaya. Wanda hakan ne ya haifar da bangar siyasa da fashi da makami da garkuwa da mutane da ɓarayin shanu da kuma uwa-uba Boko Haram.

Kwana a tituna da lunguna: – Wanda hakan ke haddasa waɗansu cuttutuka sanadiyar iska da sanyi da ruwan sama wanda duk a kansu yake ƙarewa, a ƙarshe su rasa rayukansu saboda rashin mai kula da su. Ta wani ɓangaren kuma a sace su ba tare da wani ya lura da hakan ba.

Lalacewar muhalli: Ganin yadda suke a kowani lungu da saƙo na Arewacin ƙasar ba tsafta da ƙoƙon baransu suna bin tituna da motoci, su yi ba haya a duk inda suka samu dama saboda rashin tabbacin muhalli.

Raina Hausawa daga sauran ƙabilu: Mafiya yawan ƙabilu sukan ɗauka bara da mutuwar zuciya da bautar da yara na daga cikin al’adar Bahaushe, sukan yi ma dukka al’ummar Hausa kuɗin goro.

Idan muka yi la’akari da waɗannan matsalolin, za mu ga su suka addabi Arewacin Najeriya a yau, kuma su ne maƙasudin halin da Arewa ta tsinci kanta, musamman idan muka yi duba da kashe-kashen da ake a Arewa, za mu ga da ire-iren waɗannan yaran ‘yan Arewa ake haɗa kai ake mana kisan kiyashi (domin da ɗan gari ake cin gari). Don haka, tun da bara ba addini ba ce, dole mu kawar da ita domin mu samawa kanmu salama.

Sai dai kuma kafin a kai ga kawar da bara, akwai wasu muhimman abubuwan da ya kamata gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a lamarin su magance su kamar yadda Malam Kabiru Yusuf Fagge (Anka) ya zayyano. Waɗannan abubuwa su ne kamar haka:

Da farko gwamnati ta fara tantance rabe-raben Bara da masu yin barar tun daga kan ‘yan siyasa, ma’aikatan gwamnati, ‘yan kasuwa da su kansu almajirai da miskinai da fakirai da sauran masu matattun zuciya. Ta haka ne za ta gano barar da ke da illoli ga al’umma da qasa bakiɗaya da yadda za a magance ta.

Gwamnati ta fito kuma ta tabbatar da hanyoyin magance ko rage talauci. Kayayyakin masarufi su yi sauƙi, su zama wadatattu ga al’umma. Domin a yawancin binciken da aka yi talauci ne ya haifar da wani babban kaso na ire-ren barace-baracen da ake yi.

Gwamnati ta inganta gami da zamanatar da karatun tsangayu kamar yadda gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta fara. 

Idan gwamnati ta yi haka, bana tunanin ma sai ta tayar da jijiyoyin wuya wajen hana bara, da yawa za su daina domin wulaƙanci ya fi yawa a cikinsu.

Muna fatan Ubangiji Allah ya yaye mana wannan halin da muka tsinci kanmu ciki, ya kawo mana zaman lafiya mai ɗaurewa a yankinmu na Arewa da ma ƙasa baki ɗaya. Da wannan nake muku ban kwana, Ubangiji Allah Ya haɗa muskokinmu da alheri, Amin. 

Mohammadu Bala Garba daga birnin Maiduguri a Jihar Borno ta Nijeriya. 08098331260.