Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jadadda ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na haɓaka harkokin tattalin arziƙi da inganta kiwon lafiya a Nijeriya.
Hakan na zuwa ne a lokacin da Gidauniyar Sir Emeka Offor (SEOF) ta sanar da bada gudunmawar Dala miliyan 5 ga Gidauniyar Rotary don magance matsalolin yawan mace-macen mata masu ciki a Nijeriya.
A lokacin da ya ke magana a yayin ziyarar Shugaban Amintattu na Rotary Foundation na Ƙasa-da-ƙasa, Mark Daniel Maloney a Fadar Shugaban ƙasa, Shettima ya jinjina wa gagarumar gudummawar da gidauniyar da wasu masu-ruwa-da-tsaki suka bayar ga ci-gaban Nijeriya.
Ya tabbatar da cewa a shirye Nijeriya ta ke wajen haɓaka harkar tattali, ya na mai kira ga Gidauniyar Rotary da sanya hannu wajen shawo kan matsalolin kula da muhalli da suka shafi lamuran gadun daji da makamantansu ta hanyar samar da shirye-shirye kamar aikin ‘Great Green Wall’.
Shettima ya kuma bada tabbacin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya wajen bai wa harkokin ilimi muhimmanci musamman ga matasa don ba su damar inganta kansu da kuma al’umma baki ɗaya.
A nasa jawabin, Daniel Maloney ya yaba wa ƙoƙarin gwamnatin Nijeriya a harkar kiwon lafiya musamman wajen magance matsalolin yaɗuwar cutar polio, ya na mai cewa hakan ya samu ne sakamakon ƙoƙarinta na haɗe kai da wasu ɓangarori wajen cimma nasara.
Haka ma Kodineta-Minista na Lafiya da Kula da al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya jinjina wa aikin alheri na Gidauniyar ta Rotary da Gidauniyar Sir Emeka Offor bisa gudunmawarsu, ya na mai cewa hakan zai kawo gagarumin sauyi ga rayukan al’umma a Nijeriya.
Kazalika, shi ma Sir Emeka Offor ya ƙudiri aniyar cigaba da tallafa wa shirye-shiryen gwamnati da suka shafi harkokin kula da lafiya don sauƙaƙa wa al’umma a ƙasar, kamar yadda Stanley Nkwocha, Babban Mai taimaka wa shugaban ƙasa akan harkokin Sadarwa ya bayyana a wata takarda.