Mu na fatan gwamnati ta samar wa masu buƙata ta musamman aiki – Sani Dambatta

Daga BABANGIDA GORA a Kano

An yi kira ga gwamnati da ta yi ƙoƙari wajen samar wa masu buƙata ta musamman gurabun aikin gwamnati domin su ma a dama da su.

Hakan ya fito ne daga bakin sakataren ƙungiyar masu taimaka wa masu buƙata ta musamman ta Kanawa Malam Sani Lawal Ɗambatta a wata zantawa da ya yi da wakilinmu a satin da ya gabata.

Sannan sakataren ya kuma bayyana cewa tun farkon tafiyar wannan gidauniya ta samo asali ne daga Marigayi Malam Abba Sarki da Allah ya yi wa rasuwa shekarun baya sakamakon rashin lafiyar da ta ritsa shi tare da zama ajalinsa.

Sannan ya kuma ƙara da cewa lallai wannan gidauniya ta sama wa masu buƙata ta musamman guraben karatu daga makarantu daban-daban a cikin ƙwaryar Kano.

Sannan ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu suna da yara kimanin talatin da suke karatu, sannan yanzu haka akwai ɗalibar da ake nema wa gurbin karatu a jami’a tare da waɗanda suke kusa da kammala sakandire.

Kazalika ya kuma ce lokacin Marigayi Malam Abba Sarki ne wannan gidauniya ta buƙaci majalisar dokokin jihar Kano da ta sama wa masu buƙata ta musamman dokar da za ta kula da su wajen cin zarafinsu da dukkan abubuwan da suka shafi masu buƙata ta musamman.

Sakataren ya kuma buƙaci gwamnati jihar Kano ta taimaka wajen sama wa masu buƙata ta musamman guraben ayyuka ga waɗanda suka kammala karatu tare da taimaka wa wajen karatunsu a jahar Kano.

Sani Lawal Danbatta ya koka bisa rashin haɗin kan masu buƙata tamusamman a jihar Kano bisa yadda ba su zama inda Allah ya ajesu tare da hakuri, inda kuma ya ce lallai bara ba za ta zama abin azo a gani ba garesu.

Sannan kuma ya buƙaci masu hannu da shuni da su taimka wajen taimakon masu buƙata ta musamman a jihar Kano da ma sauran gurare daban-daban.

Daga ƙarshe ya kuma bayyana cewa ƙungiyar ba ta tsaya nan ba wajen ayyukan ta, inda take taimaka wa marasa ƙarfi da marayu da sauran mabuƙata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *