Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Kwanci tashi ba wuya ga mai yawan rai, ga shi yau har azumin watan Ramadan ya kai rabi. Musulmi a ko’ina a faɗin duniya, sun shagaltu da ayyukan ibada da neman ƙarin kusanci ga Allah maɗaukakin sarki, wajen kamewa daga ci da sha da jima’i a lokacin wuni, wato daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana, da kuma yawaita karatun Alƙur’ani Mai Girma da halartar wuraren tafsiri, zikirori da nafilfili a cikin yini da dare.
Lallai babu shakka Ramadan wata ne mai tsarki da ɗimbin daraja, kuma lokaci ne na tsarkake zukata, da ƙara samun tsoron Allah. Wani muhimmin abu da malamai ke yawan kwaɗaitarwa a wannan lokaci shi ne, kyautatawa makusanta da maƙwafta da abin da Allah ya hore na daga abinci ko abin sayen abinci, musamman a wannan yanayi da ake ciki na tsadar rayuwa da rashin kuɗaɗe a hannun jama’a.
Masu hali ko mawadata daga cikin mu kan yi amfani da wannan wata na Ramadan wajen fitar da Zakka daga dukiyar da Allah ya ba su, domin rabawa ga miskinai da mabuƙata. Sai dai shin anya ana fitar da wannan Zakka yadda za ta yi tasiri wajen sassauta ƙuncin da jama’a ke ciki? Ko kuwa ana ba da ita ne ga ’yan uwa da abokan arziki waɗanda ba sa cikin jerin mutanen da ya kamata a ba su Zakka, don ganin ido da neman suna?
Na ji wani malami na ƙorafi a cikin wa’azinsa game da yadda wasu masu kuɗi ke fitar da Zakka da ɗan abin da bai kai ya kawo ba, da sunan Zakka. Har yana cewa, abin da aka bashi cikin ambulan a matsayin Zakka bai wuce kuɗin motar da ya biya ya je gidan mutumin da ya gayyace shi zuwa karvar Zakkar ba. Wasu kuma an ce rubuta sunaye ake yi na ’yan uwa da abokai waɗanda duk shekara su ne ake aikawa da kason su na Zakka da abin da bai fi cefanen wuni guda ba.
Ko da yake ni ba malami ba ne ballantana in yi dogon sharhi ko wata fatawa game da yadda ya dace Musulmi su fitar da Zakka da waɗanda Musulunci ya tsara su ne za su karɓi Zakkar, amma na san akwai malamai da za a iya neman ƙarin bayani a wajen su, ko kuma littattafan Musulunci da aka rubuta cikin harsuna daban-daban don ƙaruwar Musulmi, da nufin samun ingantattun bayanai kan Zakka da sharuɗɗanta.
Abu mafi muhimmanci da nake son jan hankalin mu a kai shi ne, buƙatar mu riqa yin abin da ya dace wajen ganin mun tallafawa mabuƙata da abin da zai sauƙaƙa musu samun abin da za su ci cikin wannan wata. Ko da ba daga Zakkar da muka fitar ba, za mu iya cirewa daga abincin da Allah ya hore mana, musamman hatsi, irin su gero da dawa, ko shinkafa da taliya da suga ko kayan shayi da kunu, bisa al’adar mutanen mu na nan. Sannan yana da muhimmanci wannan abin alheri na kyautatawa ya zama ana ba da shi ne ga ’yan uwa na jini waɗanda ba su da ƙarfi, ko maƙwafta masu ƙaramin ƙarfi, da miskinai da marayu. Yawaita yin alheri da kyautatawa ga waɗannan yanki na mutane yana da matuƙar muhimmanci a bisa koyarwar addinin Musulunci da zamantakewa ta ’yan adamtaka.
A daidai wannan lokaci ya zama dole in yaba wa ƙungiyoyi da mutanen da suke sadaukar da duk abin da Allah ya ba su wajen ciyarwa da kyautatawa marayu da mabuƙata, musamman a lokacin buɗe baki, inda za ka ga ana ta rabon abinci, da abin sha, wani lokaci ma har da ruwa, ko wani abin ƙwalama na marmari don masu azumi da ba su da halin sayen abinci, tun daga farkon Ramadan har zuwa ƙarshensa. Wannan ba qaramin aikin alheri ba ne, da yake tattare da ɗimbin lada, kamar yadda ma’aikin Allah mai tsira da aminci ya yi mana bushara cewa, koda da tsagin dabino ne a ciyar da mai azumi ko mabuƙaci da ke cikin halin yunwa.
Wannan kuma ƙarfafa gwiwa ne ga masu ƙaramin ƙarfi ba sai kana da arziki mai yawa ba, komai ƙanƙantar abin da Allah ya hore maka kana iya sayen wani abu da zai faranta ran mai azumi, daga cikin maƙwafta ko ɗan uwa da mabaraci. Bai dace ba, a ce kana da halin da za ka taimaka amma kana ganin asara ne, matarka na soye-soyen kaji da farfesu kala kala, an cika gida da ƙamshi, amma ka gaza aikawa maƙwabcinka da wani abu daga ciki, don matarsa da ’ya’yansa su mayar da yawu. Alhalin koyarwar addinin Musulunci ta zo da bayani kan yadda muhimmancin maƙwabci yake a cikin addini.
An rawaito Uwar Muminai Ummu Salama daga cikin matan Manzon Allah Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam tana cewa, watarana Ma’aikin Allah mai tsira da aminci yana gaya mata matsayin maƙwabci kan maƙwabcinsa har ta sa ran za ta ji ya ce, ko mutuwa mutum ya yi maƙwabcinsa na da gado. Abin da ke nuna mana ƙarfi da tasirin da maƙwaftaka ke da shi. Kuma wannan ya haɗa da ɗaya babban jigon wato zumunci. Ba daidai ba ne kana da halin da za ka taimakawa ɗan uwanka na jini amma saboda wani saɓani na ’yan uwantaka sai ka kawar da kan ka daga taimaka masa, ko da kuwa ka san yana cikin tsananin buƙatar taimakon, sai dai wasu bare a waje su amfana da kai ba ɗan uwanka ba. Ba a hana taimakawa wanda ba jinin ku ɗaya ba, amma an fi son a fara da makusanta.
Na lura a cikin wannan wata ana samun waɗanda ke haɗa kuɗi don taimakawa marayu da ɗinkin Sallah, daga cikin yaran ’yan uwa da na maƙwafta. Akwai wanda ake haɗa kuɗi duk shekara qarqashin ƙungiya ta haɗin gwiwa da kuma wanda mutum ɗaya ke ɗaukar wa kansa gwargwadon hali. Wannan abu ne na faranta rai sosai, kuma yana da muhimmanci sosai mu ƙarfafa gwiwar junan mu a kan haka, musamman ganin nan da ’yan kwanaki hankali zai koma kan hidimar Sallah ƙarama. Ko ba ka samu damar yin ɗinkin kaya ba, za ka iya saya musu ’yan takalma ko huluna, ko gyalalluka na mata da ɗan kayan kwalliya na yara mata da za su ji daɗin samu.
Kar mu raina aikin alherin da za mu yi wa wani daga na kusa har na nesa, kuma kada mu damu da za a raina abin da muka bayar ko za a yaba, wannan ba shi ne damuwarka ba, babban abin buƙata shi ne samun yardar Allah. Ubangiji ya karɓi aikin da ka yi da kyakkyawar niyya, ya fi maka duniya da abin da ke cikinta.
Ya Allah ka hore mana abin da za mu yi sadaka mu yi alheri ga ‘yan uwa da maƙwaftanmu. Mu sanya farinciki a zukatan marayu da nakasassu da sauran mabuƙata. Allah ka hane mu aikin riya da aikin da watarana za mu yi gori a kansa. Ya Allah ka sa duk abin da za mu aikata na zahiri da baɗini yardarka kawai muke nema a kansa ba ta waninka ba.