Mu tuna da ’yan uwa da maƙwaftanmu

Manhaja logo

Tare Da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ya zama dole a daidai wannan lokaci a ƙara yin kira ga jama’a, saboda halin da aka shiga cikin ƙasa, dangane da ƙuncin talauci da tsadar rayuwa da ake cigaba da fuskanta. Kai ka ce rubuce-rubuce da surutai da muke ta yi a baya ta bayan kunnen shugabanni suke bi, ba a sauraron kukanmu da shawarwarinmu, bisa la’akari da yadda abubuwa suke qara taɓarɓarewa, a maimakon a samu sassauci.

Lura da yadda abubuwa ke cigaba da lalacewa a cikin ƙasa, sai mutum ya fara tunanin ko ma dai wannan faɗakarwa da ake ta yi ga shugabanni da ’yan siyasa har ma da masu ilimi da masu hannu da shuni, ba ta wani tasiri, ballantana har a samu wani sauyi a rayuwar al’ummar ƙasar nan.

Amma ta wani fannin kuma idan na tuna da faɗin Allah Maɗaukakin Sarki da ke cewa, ‘Ka tunatar, lallai tunatarwa tana amfanar mumini (mai tsoron Allah).’ Sai in ji na ƙara samun ƙwarin gwiwa, na san idan wani bai ji ba, wani zai amfana. Ko ma ba wannan ba, Allah Ya ga ƙoƙarin da muka yi da zuciya ɗaya, da irin damar da muke da ita, don jama’a su ɗauki wani darasi daga abin da muke rubutawa.

Halin da ake ciki a ƙasar nan ya sa tilas mu tunatar da junanmu, musamman waɗanda Allah Ya horewa halin taimakawa su ji tausayin na kusa da su, ’yan uwa shaƙiƙai, na kusa ko na nesa, da kuma maqwafta da ake tare, Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba. A taimakawa juna da abin da aka samu dama, daga abinci ko abin sarrafawa, domin zai ɗan sassauta musu, duba da halin da ake ciki. Kada mu raina abin da muke da shi ko abin da za mu bayar, ko da kuwa sunƙin taliya ɗaya ne ko ƙwayar dabino.

Kada mu jira sai wanda ya zo ya tambaya ko ya roƙe mu, shi ne za mu tsakuro wani abu mu bashi, muna jin nauyi a ranmu. Akwai wasu mutane da suke da dauriya da kawaici, ba sa iya tambayar abu ko su yi roƙo, ko da kuwa za su mutu da yunwa ne, saboda suna gudun zubewar mutuncinsu ko wulaƙancin da za a yi musu, kafin a taimaka musu. Babu shakka mun san kowa a ƙasar nan yana jin zafin abin da ke faruwa, ko bai shafi abin da yake samu ba, ko harkokin da yake gudanarwa ba, ya shafi yadda yake gudanar da harkokinsa. Hatta waɗanda muke ganin suna kusa da gindin maganin wato kusa da gwamnati ko manyan ’yan kasuwa, su ma idan ka kusance su za ka ji suna kokawa da yadda al’amura ke tafiya.

A maimakon mu naɗe hannu mu jira gwamnati ta kawo mana tallafi, ko ta raba mana kayan abinci da kuɗaɗe, abin da mun san ba samuwa zai yi ba, sai dai a mafarki, kamata ya yi mu-ya-mu mu gano wasu hanyoyi na yadda za su taimakawa kanmu da kanmu. Maƙwafta su samar da wani tsari na yadda wannan iyali zai kawo wani abu, wancan ma ya kawo abin da ya samu, don a samu yadda kowa zai taimaki iyalinsa a ci abinci, a kai yara makaranta. Ma’aikata su samar da tsarin yadda wasu za su riƙa ragewa wasu hanya a motocinsu, zuwa inda za su isa gidajensu cikin sauqi, haka gobe ma a yi amfani da motar wani, a tafi aiki, a kuma dawo tare, don a samu sauƙin kashe kuɗin mota ko na sayen mai. Masu makarantu su ba da damar yadda iyayen yara za su riƙa adashen biyan kuɗin makarantar ’ya’yansu cikin sauƙi, ba tare da an matsa lallai sai an biya komai a lokaci ɗaya ba. Masu shaguna su ɓullo da tsarin adashin kayan abinci ga masu sayayyar kaya a wajensu, ta yadda za su samu sauqin sayen abinci ko kayan masarufi a wajensu. Haka kuma ƙungiyoyin matasa da na cigaban gari ko unguwanni, su ma za su iya yunƙurin haɗa wani abu ta hanyar karo-karo, don sayen kayan abinci da za su raba a tsakanin mambobinsu da kuma wasu marasa qarfi kamar marayu, nakasassu, da gwagwaren mata da ba su da aure, da tsofaffi marasa gata.

Waɗannan na daga cikin dabarun da aka gwada a wasu wurare kuma aka ga tasirinsu, sakamakon yadda jama’a suke fuskantar matsalar rayuwa da kula da ɗawainiyar iyali.

A yayin da ya zama dole a nan a jinjinawa wasu mutane, musamman ’yan kasuwa da masu hali, da saboda halin tausayawa da kula da yadda jama’a ke cikin wani hali, suka ɓullo da wasu hanyoyi na karyar da farashin kayan abincin da suke sayarwa, ta yadda masu ƙaramin qarfi za su samu damar saye har su ciyar da iyalansu. Na san kuna da labarin wani Alhaji Ibrahim Iro da ke Ƙaramar Hukumar Bali a Jihar Taraba, wanda karya farashin kayan abincin da yake sayarwa a shagonsa, inda aka ce sunqin taliya da ake sayarwa Naira 500 ya mayar da shi Naira 250.

Cincirindon jama’ar da suka taru don sayayya a wannan shago a ranar da aka sanar da wannan sassauci ya isa ya sa mai saurin kuka zubar da hawaye. Irin haka ta faru a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda da ke Jihar Zamfara, inda wani ɗan siyasa da yake da babban kantin sayar da kayan masarufi a yankin unguwar Hayin Maye, shi ma ya karyar da farashin kayan da yake sayarwa, don jama’a su samu sauƙin raɗaɗin da suke da suke ciki. A Jihar Gombe ma, an samu rahoton yadda wani attijiri, ɗan siyasa da ake kira Alhaji Bala Tinka, ya tara jama’a masu ƙaramin ƙarfi don raba musu kayan abinci da na masarufi, don tallafawa ga halin da ake ciki.

Waɗannan kaɗan ne daga cikin ɗimbin mutanen da suka yi wasu abubuwa na tausaya da jinƙai ga maƙwaftansu, da ’yan uwansu, da yaran aikinsu, da suke rayuwar ƙunci su da iyalansu, a jihohi daban daban na qasar nan, daga ’yan siyasa, manyan ma’aikata, ’yan kasuwa da ƙungiyoyin sa-kai. Wasu sun yi a bayyane har jama’a da dama sun sani, duniya ta ji. Wasu kuwa sun yi ne a sirrance cikin dare ko ta tura kuɗi cikin ma’ajiyar bankin wasu abokansu da ’yan uwa, ba tare da kowa ya sani ba.

Wannan shi ne manufar wannan rubutu na yau, mu ƙarfafa gwiwar waɗanda suka yi niyya kuma suke taimakawa, don tausayawa da neman yardar Allah. Mu kuma ƙara tunatar da jama’a muhimmancin samar da dabaru da hanyoyin da za su tallafawa kawunansu, ba sai wani ya kawo musu ɗauki daga wani waje ba. Sannan kuma mu tunawa gwamnatocin jihohi da su ji tsoron Allah, su tausayawa jama’ar da suke yini cikin rana don su zaɓe su zuwa ga kujerun da suke zaune yanzu, su samar da kayan tallafi kamar yadda shugaban ƙasa ya yi alƙawari, a daidai lokacin da ake kan gaɓar wannan wahala ba sai lokacin siyasa ba. Hakan ne zai kare mutuncinsu, ya kuma tsare kujerar su.

Bisa ga dukkan alamu wannan ita ce rayuwar da muka samu kanmu a ciki, kuma bisa ga dukkan alamu mawuyaci ne a koma irin rayuwar baya, sai dai mu samarwa kan mu mafita, mu ƙirƙiro da wata salon rayuwar da za ta dace da tafiya da kowanne sauyi ya zo, wato abin da a turance ake ce wa ‘The New Normal.’ Dama a wani rubutu da na yi a baya na taɓa gaya mana muhimmancin shiri don irin sabbin canje-canje da za mu riƙa gani, saboda sauyin sabuwar gwamnati da tsare-tsare da za ta ɓullo da su. Wannan na daga cikin abubuwan da za su faru.

Fatan da za mu yi shi ne, Allah ya sa duk wani sauyi da zai zo mana, ya zo da sauƙi, kada ya sake jefa mu cikin wani ƙuncin. Kuma duk sauyin da zai tunkaro mu Allah Ya sa ya zama alheri ne ga rayuwarmu da ta iyalinmu. Muna addu’ar ubangiji ya ba mu jarabawa mai sauƙi da imanin mu da ƙarfin juriyarmu za su iya ɗauka!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *