Mu ’yan Kannywood muna da tsarki kamar ruwan zamzam, inji Halima Atete

“Dalilin da ya sa ban taɓa tsoma kaina a rigimar Kannywood ba”

Daga AISHA ASAS

Sananniyar jaruma a masana’antar Kannywood kuma mai shirya fim, Halima Atete, ta shigo masana’antar tun shekaru 10 baya, kuma za mu iya cewa, ta shigo da ƙafar dama, duba da irin nasarori da ta samu, ciki kuwa har da sarautar masana’artar wato ‘Sarauniyar Kannywood” da ake yi mata laƙabi da ita. A zantawarta da Jaridar Blueprint, jarumar ta bayyana cewa, a yanzu ta cika burinta a masana’antar, ta na mai cewa, kwalliya ta riga ta biya kuɗin sabulu a zaman da ta yi a cikin Kannywood. Don haka burinta a yanzu kawai shine ta ga ta shige daga ciki (aure), tun da ta gama rayuwar fim lafiya, ba tare da wasu ƙalubale ba. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Mene ne matsayin da kika taka a masa’antar Kannywood?
To, zan iya cewa na taka rawa mai girma a masana’antar, domin na taka rawa a manyan finafinai masu yawa, waɗanda manyan jarumai suke ciki, kamar Jarumi Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Aisha Aliyu, Rahma Sadau, Jamila Nagudu, Fati Washa, Hafsat Idris da sauransu. Hakazalika na yi nasarar hawa kowanne matsayi aka ba ni a finafinan; kamar ‘yar sanda, direbar babbar mota, kai har ma rol ɗin maza na taɓa hawa a cikin shirin ‘Mata Maza’, da dai ire-irensu da ke tattare da ƙalubale. Don haka zan iya cewa, ba abinda ya fi dace wa na yi face godiya ga Allah maɗaukakin Sarki. In kuma gode wa abokanan sana’a da kuma masoya da suke ba ni ƙwarin gwiwa ta hanyar saƙoƙinsu da kuma bibiyata ta kafafen sada zumunta da kalamai masu daɗi na jinjina.

Shekaru tara da suka gabata, na tattauna da ke a a Otal na Green Park lokacin da kika je ɗauka wa Ahmad Bifa fim ɗin ‘Al-mooru’. Nan da nan mu ka kammala tattaunawar saboda ba ki shahara ba, amma yanzu kusan za a iya kiranki da tauraruwa mafi ƙwarewa a Kannywood; ko ya hakan ta kasance?
Na gode da ka tuna min waccan tattaunawar. Kar ka manta lokacin da aka yi hirar Hadiza Aliyu Gabon ta zo ta yi wasu bayanai, amma batu na gaskiya Halima Atete yanzu da aka sani ta kasance mai nasara a fagen shirya finafinai wato ɗaukar nauyi. Na shirya finafinai kamar su ‘Daga Murna,’ da kuma wasu da dama da suka haɗa da babban jarumi a masana’antar Kannywood, jarumi Ali Nuhu. Kuma Ina daga cikin waɗanda suke da ƙarfi a masana’antar. A yau muna kafaɗa da kafaɗa da jaruman da na ke sha’awar kallon finafinan su a kafin in faɗa cikin harkar. Da dama daga cikin su idan mu ka gama aikin fim sai ka ga sun zo sun same ni su ce min “gaskiya Halima kin ba mu mamaki yadda kika yi ƙoƙari haka, gaskiya ke jaruma ce ta daban.” Ni a ganina wannan ba wani abu ba ne illa ɗaukaka daga Allah.

Wane irin ƙalubale kika fuskanta?
Lokacin da na shiga masana’antar Kannywood, tsoro da rawar jiki ya kama ni sanda aka ɗora min kyamera, da kuma lokacin da aka ce min zan yi aiki da babban jarumi ko wata babbar jaruma a masana’ar, amma nan da nan sai na saba. Bayan nan kuma abokan sana’ata suna da matuqar haɗin kai, saboda haka sun taimake ni har na kai wannan matsayi. A yau Ina kamar direbar babbar mota a harkar fim, Kallabi, wanda ‘yan fashi suka kamani a cikin fim, na fito a matsayin kwamandar sojoji; a matsayin Mata Maza a wani fim da Marigayi Rabilu Musa Ibro ya fito a mahaifina, saboda shi raggo ne a fim ɗin, idan ya taro faɗa ko abinda ya fi ƙarfin shi ko makamancin haka. Sai na taka rawa akan hatsabibiya maras jin magana. Haka kuma bayan fim ɗin, sai na fahimci cewa ku maza kun fi mu morewa, daboda za ku iya fita da wandon jins ɗin ku, ku fita wajen wasanni da fita yin rawa da abokai da kuma sauran abubuwan da mata ba sa iya yi. Saboda haka gaskiya Ina matuƙar jin daɗin yin abu tamkar namiji; abin jimami kuma sai aka zo mahaifin na wa a fim Rabilu Musa Ibro ya yi mutuwa ta haƙiƙa. Allah Ya saka masa da gidan Aljanna.

To, zuwa yanzu mene ne Halima Atete za ta iya nunawa a matsayin ribar fim?
To, gaskiya yanzu dai ba zan iya cewa ga yawan finafinan da na fito a cikin su ba, domin suna da yawan gaske, amma akwai irin su ‘Mata Maza’, ‘Kallabi’, ‘Wata Huɗu’, ‘Ɗakin Amarya’, kai gaskiya finafinan fa da yawa. Saboda haka masu ruwa da tsaki a harkar Kannywood da ke arewacin Nijeriya suka haɗu suka naɗa ni a matsayi ‘Sarauniyar Kannywood’ inda kuma Masarautar Zamfara suka shirya min ƙayatacciyar liyafar naɗin. Na gina gidana na kaina, ina da mota, sannan asusun bankina ba tagajan-tagajan ba ne kuma ina da masoya a faɗin ƙasar nan. Allah ya wadata ni da ƙoshin lafiya, Ni Musulma ce; kyakkyawa son kowa. Na kuma samu damar zuwa ƙasa mai tsarki na yi aikin Hajji. Saboda haka babu abinda nake da buri yanzu da ya wuce in ga na ci lokaci na lami lafiya.

Da abubuwan da kika cimma cikin shakara 10 a masana’antar Kannywood wanda wasu ba su same shi ba, yaya kika yi da maƙiya kuma? 
Eh, dukkanmu muna da maƙiya, amma Ni kodayaushe nakan tabbatar na yi addu’a sai in bar sauran a hannun Allah. Ka san ko kai ba kowan-kowa ba ne a rayuwa, duk da haka sai ka samu maƙiya da mahassada, amma kodayaushe Ina jin haushin yadda mutane suke faɗar wasu maganganun akan mu. Ina so mutane su fahimci yawanci cewa yawancin abubuwan da muke yi a cikin fim ba gaske ba ne, muna faɗakarwa ne da wayar da kan mutane, kamar a fim ɗin ‘Mata Maza’, na fito mai karsashi a jiki kuma da shiga maza. Saboda haka, ba zai yiwu ba in yi irin wannan shigar a gaske, mu ma kamilallun mutane ne kuma natsattsu kamar kowa, muna da laushi kamar soso, kuma mu masu tsarki ne kamar ruwan zam-zam. Saboda haka mutane ka da su ji shakkar tunkarar mu da maganar aure, kuma ba za su yi da na sani ba idan an yin. Ma yi maku alƙawari, duk da cewa ni mace ce mai tsananin kishi kamar yadda nake a shirin fim ɗin ‘Ɗakin Amarya’, lokacin da mijina Ali Nuhu ya ƙaro aure, Aisha Aliyu Tsamiya, inda na kusa cinna wa gidan wuta kawai a fim. Kuma wannan fim ɗin ya haɗa ni da mutane da dama, musamman mata, saboda na taka fawa mai kyau a fim ɗin. Dukiya irin su babban tv na bango da ka ga na fasa shi duk da gaske ne, da mai kyau ne fil; haka shi ma raunin da ke hannuna gaskiya ne. 

Na yi tunanin ki sako zancen aure a bayanan ki na baya. Hakima, kina da kyau, kin kasance mai sa’ar rayuwa, haka zalika kina da rufin asiri, uwa uba tarin masoya da kike da su. Ta ya aka yi ba mu ji zancen aurenki ba?
Da farko dai ni ina son ‘ya’ya, ina so in yi aure, in haihu. Ina da burin tarbiyyatar da ‘ya’yana kan hanya madaidaiciya tare kuma da kula da mijina. In kafa kasuwancin da zan dinga kula da shi, sannan in tsunduma karatun addini, don ganin na miƙa wuya ga bautar Ubangijina yadda ya kamata. Wannan shine burina a yanzu. Zancen manema da kake yi kuwa, ina da su tari-tari, sai dai ina bin abin ne kan tsari, tamkar dai wasan ƙwallon ƙafa, ina saka ido ne don gano wanda ya fi kowa a cikin maneman, wanda zan ba wa zuciyarta har alaƙar ta kaimu ga aure. Sai dai a halin yanzu, ba ni da sunan wannan gwanin na wa. Hakan ne ta sa ba ni da ranar da zan iya faɗa a matsayin ta aurena. Babban ƙalubalen da mu ka fi fuska shine, irin kallon da al’umma ke mana, a matsayin ballagazun mata. Wannan ta sa da yawa masu zuwa neman, sukan zo ne da wannan fahimtar, a lokacin da suka fahimci ba haka mu ke ba, sai a neme su a rasa.

A cikin shin fim ɗin ‘Kongari’, kin fito a matsayin karuwa kuma Magaji. Kuma wannan rawar da kika taka ta fita sosai, tamkar dai ta karuwar gaske. Ko ya aka yi kika samu wannan ƙwarewar?
To, wannan lokaci ne mai tsayi a can baya. Kuma na ji daɗi da ka ce na samo rol ɗin yadda ya dace. Yanzu haka ina tunanin kafa gidauniya, ta taimakon mata zawarawa da kuma waɗanda mazajensu suka mutu. Kuma wannan gidauniyar zan yi ta ne don mutane na, kamar yadda ka sani, ni ‘yar Maiduguri ce, ɗiyar mutan Borno ba. To wannan gidauniyar dai da na ke ƙuduri ta su ce. Sai zance na gaba, wanda na san ba za ka kai ƙarshen wannan tattaunawar ba tare da ka yi mun tambayar ba, don haka bari in sanar da kai tambayar da amsar bakiɗaya. Na san za ka tambaye ni, me ya sa a duk lokacin da na fito a matsayin matar jarumi Ali Nuhu, na ke shagaltar da masu kallo, kuma fim ɗin yake samun karɓuwa. To amsar dai itace; Ali Nuhu mutum ne da ya taimaki mutane da yawa a masana’antar finafinai, da yawa sun samu ɗaukaka ta sanadiyyar sa, wannan ce ta sa Allah ke ɗaukaka shi a kowanne lokaci. Babu wata alaƙa da ke tsakaninmu da ta wuce ta mutunta wa, fahimtar juna da kuma kasancewar mu ‘yan gari ɗaya. Bayan haka kowa ya sani fuskar Ali Nuhu na siyar da finafinai tamkar mayunwacin da ya ga nama.

Mu koma ɓangaren sutura. Me ya sa kika fi sha’awar sa kaya matsatsu da suke bayyana surar jikinki. Shin ko kina aika saƙo ne ga maza ‘yan bariki?
Ba laifi ba ne idan mace ta nuna wa duniya ita kyakkyawa ce. Ko na bayyana surata ko ban bayyana ba, da ka kallan ka san ina da ababen da za a so. Duk da cewa ina taka-tsantsan da irin kayan da zan sa. Sai dai abin da na ke so ka fahimta, saka wando ko matsatsun kaya a fim ya rataya ne ga shi mai shirya fim ko mai bada umurni, domin su suke zaɓa mana kayan da za mu sa. Kaga kuwa ba abu ne na sa kai ba. Ni Musulma ce, wadda ta fito daga gidan tarbiyya. Don haka ina ƙoƙarin ganin ban ƙetare iyakar da addinina ya shar’anta ba.