Muhammadu Sanusi ya hango wa Nijeriya tarnaƙin ƙura gabanin zaɓen 2023

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Sarkin Kano mai murabus, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya yi hasashen tarin ƙalubaloli da Nijeriya za ta fuskanta gabanin zaɓen shekara ta 2023, yana mai cewar, akwai buƙatar ‘yan takara su yi kyakkyawan shiri domin tunkarar su.

Sanusi ya kuma fahimci cewar, ƙasar ta Nijeriya tana zaman bakin kogi ne da lokacin irin wannan zama ya ƙure.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriyar dai yana jawabi ne a garin Abeokuta ta jihar Ogun, a wani taron liyafa na cika shekaru 80 da rayuwar wani babban basarake, Babanla Addini Mai Ƙasar Egba, Chief Tayo Sowunmi.

Tsohon Sarkin na Kano dai wanda a yanzu shi ne Khalifan Ɗariƙar Tijjaniyya a ɗaukacin ƙasar ta Nijeriya, ya kuma yi waiwaye da tunin cewar, Nijeriya ta fuskanci makamancin yanayi da ya yi hasashe, amma yance rux’ɗanin ƙalubale da yake gabanin zaɓen shekara ta 2023 ya shige kwatancin na shekara ta 2015.

Sunusi, don haka sai ya gargaɗi masu fafutukar neman shugabancin ƙasar nan, da su yi kaffa-kaffa da ire-iren ƙalubaloli da za su iya tasowa, domin kuskuren rashin lura da matsalolin zai jawo wa ɗaukacin ‘yan ƙasa ɗimbin wahalhalu.

“Masu fafutukar neman shugabancin ƙasar nan za su fuskanci ƙalubaloli masu yawan gaske, ina fatar zasu fahimci cewar, matsalolin da za su fuskanta a cikin wannan fafutuka, yawan su sun nin-ninka waɗanda aka ci karo da su a shekarar zaɓe ta 2015, don haka ya zama wajibi ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya su ja ɗamara domin tunkarar wannan ƙura.

“Amma shawo kan waɗannan ƙalubaloli ba yana nufin kowane ɗan ƙasa ya tsumduma cikin harkokin siyasa ba ne, haƙiƙa wannan ƙasa tana buƙatar gogaggun ‘yan siyasa, tana buƙatar limaman addinin Musulunci da na Kiristanci, waɗanda za su yi tsayin daka, suna tunawa ‘yan siyasa buƙatar aji tsoron Allah Mabuwayi.

Sunusi ya ce ba shi da niyyar tsayawa takarar shugabancin ƙasa a zaɓe mai gabatowa, yana mai cewar, ya gamsu da wannan jagoranci na ɗariƙar tijjaniyya da Allah ya ba shi, musamman ma da ya ke ya taka rawa a fannoni daban-daban na rayuwa a can baya, kuma zai cigaba da yi wa Allah godiya bisa waɗancan damarmaki da Mahalicci ya ba shi.

Duka waɗannan bayanai sun biyo bayan tambaya ne da kakakin masarautar ta ‘Egbaland’ ya yi wa Sunusi na cewar, ko ‘yan Nijeriya za su jira shugabancin ƙasa daga Muhammad Sunusi a zaɓe mai gabatowa?

Sowunmi dai, a can baya shi ne jami’in hulɗa da jama’a a ofishin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Sowunmi ya ce wa Sunusi, “an buƙace ni ne na tambaye ka, ko za mu sanya ran samun shugabancin gwamnatin siyasa daga gareka a nan gaba. Ko ina da amsar wannan tambaya, ni kaina ban sani ba. Amma abu guda dana shaida masu shi ne, matuƙar kana raye, ina da damar faɗin cewar, matuƙar kana raye, za ka kasance ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa, ɗan Nijeriya da baya ƙyamar kowa, shugaban shugabanni, mai riƙon addinin Musulunci, Shugaban Ɗarikar Tijjaniyya, kuma haske mai kore duhu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *