Mulkin Buhari: Demokraɗiyya ko mulkin mallaka?

Daga NAFI’U SALISU

An daɗe ana ruwa ƙasa tana shanyewa. A yau shekaru 63 da Nijeriya ta samu ‘yancin kai daga Turawan mulkin-mallaka, amma har yanzu ɗan Nijeriya bai bambance tsakanin mulkin-mallaka da mulkin dimokraɗiyya ba, sakamakon rashin iya shugabanci ko kuma dai rashin sanin kima da mutuntakar ‘yan ƙasa.

Idan muka kalli yadda tsarin tafiyar da mulkin shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari yake tafiya, zamu iya cewa gara jiya da yau. Domin kafin zuwan wannan Gwamnatin ta Buhari a shekarar 2015 zuwa yau, ‘yan Nijeriya suna gudanar da rayuwarsu cikin sauƙi, don kuwa kayayyaki da kayan masarufi na abinci suna da sauƙin samuwa ga ‘yan ƙasa, amma a cikin wannan Gwamnati ta Buhari, sai gashi an wayi gari kayayyaki sun yi tashin gwauron zabi (musamman kayan masarufi) wanda tun kafin hakan ma, da yawa wasu talakawan ƙasan su kan sha wahala wajen samun abin da za su saka a cikinsu.

Abubuwa da dama sun faru a cikin wannan Gwamnati ta Buhari, kuma a kullum babu tausasan kalamai ga ‘yan ƙasa don nuna tausayawa a gare su daga shugaban ƙasa, sakamakon haka sai kalaman da suke ƙona ran ‘yan ƙasa.

Tun bayan zuwan Gwamnatin Maigirma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, talakawan Nijeriya suke sa ran samu canjin rayuwa, daga rayuwar qunci da halin ni ‘yasu, zuwa kyakkyawar rayuwa mai cike da walwala gami da farin cikin da zai tabbatar da samun ‘yanci wurin ‘yan ƙasa.

To sai dai har yanzu da muke cikin shekara ta takwas a cikin Gwamnatin Buhari, talakan Nijeriya bai samu wancan farin cikin da yayi tsammanin samu ba, wanda kuma saboda kwaɗayin samun farin cikin ne yasa talakawa suka kafe tare da dagewa a kan ganin Muhammadu Buhari ya samu kujerar shugabancin wannan ƙasa, har kuma Allah Ya tabbatar da hakan a shekarar 2015.

Kafin zuwan Maigirma shugaban ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari a shekarar 2015 ya zamo shugaban ƙasa, an sha jin yadda yake fitowa a kafafen yaɗa labarai da jaridu yana faɗin maganganu a kan shugabannin Nijeriya, tare da faɗar ire-iren abubuwan da ya dace suyi a kan mulki, da kuma nuna jin zafi a kan yadda ake mulkar talakan Nijeriya. An kuma sha jin yadda Buhari yake kushe shugabanni a kan rashin iya tafiyar da mulkin ƙasa, wanda yake ganin ya hana samun kyakkyawar rayuwa ga ‘yan ƙasa.

Duk waɗancan ɓaɓatu da Buhari ya riƙa yi a baya a kan abinda yake kira da haƙƙin talaka, abin dai bai canza zani ba a yanzu da yake zaman shugaban ƙasar Nijeriya, wanda saɓanin haka ma sai ƙara lalacewa da abubuwa suka yi, rayuwa ta tavarvare, ‘yan ƙasa suka shiga cikin mawuyacin halin da suka fita cikin hayyacinsu. Kowa ya gani kuma ya shaida yadda rayuwa tayi tsada, duk wani abu da talaka yake samunsa a cikin sauƙi a da, a halin yanzu yafi ƙarfinsa, sai dai ɗan abinda ba a rasa ba.

Duk da cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sha nuna adawa ga gwamnatocin baya a bisa yadda suke tafiyar da mulkinsu, kuma suka sha suka daga gare shi, a lokacin da suke shugabanci talakawa ƙasa suna gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da salama.

Sannan duk da yadda ake ganin ana yin zalunci da tauye haƙƙin ‘yan ƙasa, amma kuma ‘yan ƙasa suna cikin salamar da take basu damar zuwa gonakinsu domin yin noma, suna da kwanciyar hankalin da suke zuwa kasuwanni, suna da kwanciyar hankalin da suke sadar da zumunci ga ‘yan’uwa a duk nisan garin da ‘yan uwansu suke.

Idan muka kalli wani ɓangaren, masana tattalin arzikin ƙasa sun sha fitar da bayanai a kan irin maƙudan kuɗaɗen da Nijeriya ta tara a wannan zamanin na mulkin Muhammadu Buhari, amma kuma lalacewar ƙasar yafi na lokacin da ƙasar bata samun kuɗin shiga kamar na yau. Haka nan shugaba Buhari ya sha faɗin cewa shugabannin baya sun lalata ƙasar nan da bashin da suke ciyowa daga ƙasashen ƙetare, sai gashi yanzu ana bin Nijeriya kuɗin suka wuce mizani da aka ciwo bashinsu a wannan Gwamnatin ta Buhari.

Lokacin da farashin kayan abinci ya tashi, ‘yan Nijeriya sun shiga cikin ruɗani musamman talakawa, waɗanda suke shan wuya kafin su sami abinda zasu ci su rayu. Da ‘yan Nijeriya suka riƙa maganganun nuna damuwa a kan tashin kayan masarufi, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi maganganu a kai, kuma maganganun nasa basu nuna tausayawa ga ‘yan ƙasa ba.

Haka nan lokacin da kashe-kashen al’umma da garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa ya yawaita a Arewacin ƙasar nan, kullum shugaban ƙasa yana ikirarin ana yaƙi da ‘yan ta’adda kuma ana murƙushe su, har aka wayi gari shugaba Muhammadu Buhari yazo yana maganar cewa wai ya cika alƙawurran da ya ɗaukar wa ‘yan Nijeriya. To wataƙila hakan ne, domin zai iya cika su a takarda amma dai a zahiri a bayyane ‘yan ƙasa basu shaida hakan ba.

Idan muka koma kan batun canjin kuɗi kuwa, akwai wani abu da yake da matuƙar ɗaure kai da kuma yake bai wa ‘yan ƙasa mamaki. Gwamnatin Buhari ta fito da zancen canza fasalin takardun kuɗi ba tare da yin la’akari da yadda ‘yan Nijeriya zasu shiga cikin mawuyacin hali ba, haka nan kuma ba a yi la’akari da yadda rayuwar ta canza ba, wanda ya jawo tsadar rayuwa da rashin aikin yi ga ‘yan ƙasa. Koda yake dama a baya shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fito yana bayyana cewa babu aikin da zasu iya baiwa ‘yan ƙasa, kuma duk wanda yake jin yunwa yaje gona ya nemi abinci.

To amma da yake wannan maganganu ya kasa tuna yadda noma ya zamo masifa a yankin Arewacin ƙasar nan, domin dai ko bai zo yankin ya ganewa idonsa ba, labarai daban-daban sukan je masa na yadda ‘yan ta’adda suka mamaye yankunan Arewa suke kisan gilla ga manoma, wanda kuma hakan ya zamo tarnaqi da ƙalubalen hana zuwa gona ga manoma. Mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu wajen noma abincin da ‘yan ƙasa zasu ci.

Na tabbatar batun canja fasalin kuɗin ƙasa ba an yi shi ba ne don talakawan Nijeriya su amfana ko su ji daɗi ba, domin ina talaka ma yaga kuɗin ballantana har ya tara su, wanda kullum sai talaka ya fita neman abinda zai ci da iyali. Kuma a talakawan ƙasar nawa ne suke aikin Gwamnati? Mafi akasarinsu leburori ne da suke da ƙaramin ƙarfin samun abinda zasu gudanar da rayuwarsu.

Gwamnatin Buhari bata yi wannan canji don talaka ya ji daɗi ba, kawai an yi ne don wata manufa ta daban. Duk da cewa da maganganu suka yi yawa Gwamnatin Buhari ta bayyana cewa an yi wannan canja fasalin kuɗi ne domin ayi maganin ɓarayin ƙasa, a kuma daƙile ayyukan masu garkuwa da mutane. Wannan rainin wayo ne kawai ake yi wa ‘yan ƙasa, domin wannan sam!

Ba hanyar da ya kamata a yi amfani da ita be idan har anyi niyya kuma ana son ayi maganin ɓarayin ƙasa da masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa. Ita Gwamnatin tafi kowa sanin hanyoyin bi wajen magance satar kuɗin ƙasa da kuma yaƙi da ‘yan ta’adda tare da kawo ƙarshensu.

Yau shekara nawa ana ɓaɓatun yaƙi da ta’addanci a Nijeriya ƙarƙashin wannan Gwamnatin? Gwamnatin da har yanzu ɗan Nijeriya bai mori komai a tare da ita ba sai baƙar wahala da ta haifar da matsananciyar tsadar rayuwar da ta saka ‘yan ƙasa cikin mawuyacin halin da wasu ma basa bambance tsakanin mutuwa da rayuwa?

Ya kamata a ce Gwamnati ta yi la’akari da su waye waɗanda take son ta yaƙa a ƙasar nan don magance satar kuɗin ƙasa. Shi Gwamnan babban bankin ƙasar ai yana da kashi a gindi, domin a lokacin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗauko shi ya kawo shi a matsayin Gwamnan babban bakin ƙasa CBN, akwai zargin badaƙalar kuɗin da ake yi masa, sannan kuma ya faɗawa shugaba Buhari cewa ba zai yi aiki da duk wanda yayi aiki tare da tsohon Gwamnan babban bankin ƙasa CBN Sunusi Lamiɗo Sunusi ba, kuma Buhari ya amince da hakan, abin da ya jawo sallamar kowa da yayi aiki ƙarƙashin Malam Muhammadu Sunusi Lamiɗo Sunusi ll.

Sannan da aka yi canjin fasalin kuɗinnan, Gwamnan babban bankin ƙasa Emifele ya tabbatarwa da ‘yan ƙasa cewa sun buga isassun kuɗaɗen da za su wadatu a cikin ko’ina a ƙasa, amma yau me ya faru da aka zo kan gavar daina amfani da tsaffin kuɗin? Har yanzu babu isassun kuɗin a bankunan ƙasar nan, haka nan idan kaje POS ma babu.

Hakan kuma hakan ya kawo tsayawar hada-hadar kasuwanci a ƙasa, yayin da wasu kuma suke yin amfani da wannan suna cin karensu babu babbaka. Sannan idan kaje ƙauyuka zaka samu cewa mutane suna cikin mawuyacin hali. Domin akwai ƙauyen da idan suka kawo niƙan hatsi inji, to sai dai su ɗibi hatsin su bayar a matsayin kuɗin niƙan.

Yayin da suma masu injinan suke buƙatar kuɗin, amma dole haka suke haƙura su karɓi hatsin a madadin kuɗi suyi wa mutane niƙa.

To yanzu dai gashi mun ga yadda wannan canja fasalin kuɗi ya haifar da sabuwar rashawa da cin hanci, a sakamakon rashin isassun sabbin takardun Naira ya jawo mutane yin tururuwa a bankuna don samun sabbin kuɗin amma babu. Hakan tasa wasu suka riƙa karɓar dubu goma na tsohuwar Naira suna bayar da dubu takwas na sabbin kuɗi ga wanda yake buƙata.

An ce an sauya kuɗin ne don a daqile maguɗin zaɓe ga ‘yan siyasa saboda zaɓen 2023 dake ƙaratowa, to amma kuma anga yadda ‘yan siyasar suke bin gida-gida suna karɓar katin zaɓe a hannun mata ana basu kuɗi ana kwafe wasu lambobi dake jikin katin.

Sannan an ga yadda ake kwasar sabbin Naira ake kaiwa attajirai har gida, shi yasa duk inda ka zaga-ka-zago a bankuna zaka iske duk talakawa ne suke bin layin cirar kuɗi, domin ko ni kaina wallahi ban tava ganin maikuɗi a layin neman karvar sabbin kuɗin Naira da aka canzawa launi ba.

Idan ma wai shugaba Buhari yana nufin zai karya attajiran ƙasar nan ne da yake kira da ɓarayin ƙasa, to mu sani cewa wannan wasan kwaikwayo ne kawai. Idan ma yana son ya nunawa duniya cewa akwai ɓarayin ƙasa da suka sace kuɗin ƙasa, to me zai hana ya bayyana sunayensu ga ‘yan Nijeriya, ko kuma ya haɗa su da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC idan har gaskiya ne.

Don haka ni ina tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewa, wannan batun canjin kuɗin na Gwamnatin Buhari ba komai ba ne face lauje cikin naɗi, domin akwai abubuwan da ‘yan Nijeriya suke buqata ba canji kuɗi ba, tunda gashi canjin kuɗin bai zamo alheri ga talakawa ba.

Su kuma masu kuɗi ko a jikinsu, domin idan ma baku sani ba kowa ya sani, duk waɗannan gine-ginen plaza-plazar da sabbin gidajen mai, da kamfanoni (musamman na sarrafa shinkafa), to duk ana gina su ne ba don ci gaban ƙasar nan ba wallahi-tallahi, domin ire-iren waɗancan kuɗaɗen ne da aka sata na ‘yan ƙasa ake bubbuɗe waɗannan wuraren, shi yasa ku ke ganin kasuwanci yana ƙara lalacewa baya ci gaba.

Za ku yarda da abinda nake faɗa muku idan ku ka yi la’akari da tarin yawan masana’antun da aka samar na sarrafa shinkafa da sauran kayan masarufi, amma abincin har yanzu yana matuƙar tsada. Sannan ga sabbin gidajen mai ana buɗewa amma kuma har yanzu mai yana wahala.

To idan duk an yi ne domin a bunƙasa ƙasa, me yasa abinci yake tsada? Me yasa mai yake wahala ‘yan ƙasa suna shan wuya? Me yasa da aka yi canjin kuxi talakawa ne kawai suke bin layin neman sabbin takardun kuɗi a bankuna? Don haka kowa ya dawo cikin hayyacinsa ya fahimci manufar wannan Gwamnati.

An lalata ilimi, karatu ya gagari ɗan talaka a Nijeriya. Haka nan ɓangaren zuwa aikin Hajji sai dai Attajirai ne suke ta zuwa suna ƙara maimaitawa don talakawa abin yafi ƙarfinsa ma. An sakawa mutane talauci da fatara, har an kai gaɓar da mutane basa tunanin haƙƙoƙinsu dake hannun Gwamnati, kullum fafutukarsu ta abinda zasu ci ne, amma abin da suke nema suci ɗin ma an hana su nemansa cikin salama, to ya ake su talakawa suyi.

Sannan kun ji shi shugaba Buhari da shugaban rundunar sojojin ƙasa Faruq Yahaya sun fito suna shelar sojoji za su ɗauki mataki ga duk wanda ya ce zai tada hankali a ƙasa. Duk me ya kawo wannan? Sabida an san ba a shuka abin alkairi ba, domin an daki mutane ba zai yiwu kuma a ce za a hana su kuka ba.

Babban abinda yake bani baƙin ciki da takaici, bai wuce yadda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya fito yake faɗin cewa, wai ‘yan Nijeriya basa yaba masa a kan abubuwan raya ƙasa da yake samar musu. Abinda duk yake damun al’umma ba shi ne a gabansa ba, domin kullum hare-haren ‘yan bindiga da yin garkuwa da mutane yana ƙara yawaita, amma kafin ka ji yayi maganar dakile hakan ko ɗaukar mataki za a daɗe.

Idan akwai abinda ‘yan ƙasa suka fi buƙata bai wuce abubuwa guda biyu ba, na farko shi ne samar da tsaro, a kawo ƙarshen ta’addanci a ƙasar nan, ta yadda duk inda za mu shiga ba mu da wata fargabar za a tare mu a buɗe mana wuta, ko kuma a kwashe mu a yi daji damu a nemi kuɗin fansa.

Abu na biyu kuma shi ne, a samar da hanyar sauke farashin abinci ta yadda ‘yan ƙasa za su iya sayen kayan masarufi su ajiye a gida. Waɗannan abubuwan biyu kaɗai idan da Gwamnatin Buhari ta samar da su ga ‘yan ƙasa, to da sai mu ce sambarka.

Don haka ina kira ga ‘yan ƙasa lallai mu tabbatar tun daga sama har ƙasa mun zaɓi mutanen kirki waɗanda za su gina mana ƙasa da ayyukan alkairi, ba waɗanda zasu cika mana shafukan jaridu da kafafen watsa labarai da surutai ba. Kuma zuwa wannan lokaci jikin Ta-ƙaura ya yi la’asar, don haka, jiki magayi.

Nafi’u Salisu
Marubuci/manazarci
Ya rubuto daga jihar Kano
Email:[email protected]
08038981211