Mun ƙulla ƙawance da BBC Hausa ne saboda shahararsu – Shugaban Qausain TV

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Kamfanin Yaɗa Labarai na Qausain TV, Alhaji Nasir Musa Idris, wanda aka fi sani da Albanin Agege, ya ce sun zaɓi gidan rediyon BBC Hausa ne domin ƙulla ƙawance saboda shahararsu da ingancinsu ta fuskar yaɗa labarai a faɗin duniya.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin wata hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa a lokacin da ya kai wata ziyarar aiki a sashen Hausa na BBC dake birnin Landon a ƙasar Birtaniya ƙarshen wannan makon.

Nasir Musa ya ce tashar tasu wadda ke kan tauraron ɗan Adam na Eutelsat 16 A, ta zavii haɗin gwiwa da BBC Hausa ne domin ƙara inganta shirye-shiryen su, wadda dama ya ce tuni al’umma ke dakon jiran tashar Qausain TV, sakamakon kyawawan shirye-shiryen da suka bambanta da sauran tasoshin TV a faɗin Nijeriya.

“Mun fara yayxa shirye-shiryen mu tun a ranar 1 ga Watan Oktobar 2021, waɗanda suka haɗa da labarai, rahotanni, siyasa, nishaɗi, al’adu da addini da sauransu. Kuma babban abin sha’awa shi ne yadda muka ɗauki harsuna 3 domin ƙawata shirye-shiryenmu da su, inda muka bai wa harshen Hausa kashi 70, sannan turanci da Larabci kaso 15 kowannensu,” inji shi.

Da aka tambaye shi game da ƙalubalen da tashar ke fuskanta, Nasir Musa Idris, ya bayyana rashin wutar lantarki da rashin ƙarfin intanet da kuma ƙarancin tallace-tallace a matsayin manyan ƙalubalen da tashar ke fuskanta.

Yana mai cewa kamfanin na kashe maƙudan kuɗaɗe wajen gudanarwa, musamman ɗyawainiyar man dizel da biyan albashi da sauransu. Amma ya ce kawo yanzu an fara sanin tashar, kuma suna fatan fara samun tallace-tallace domin samun damar yaɗa manufofin da suka jima suna ci wa Arewa tuwo a ƙwarya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *