Mun cika alƙawuran da muka ɗauka wa ‘yan Nijeriya – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A cikin jawabin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya yi a wurin taron bitar ayyukan da gwamnatin sa ta aiwatar wa ‘yan Nijeriya, Shugaba Buhari ya ce an aiwatar da ayyuka masu tasiri a faɗin ƙasar nan, waɗanda suka cika buri da muradin ‘yan Nijeriya.

Wannan taro na musayin ra’ayoyi ne da kuma yin bitar ayyukan da gwamnati ta aiwatar a tsawon shekaru 7 a Nijeriya wanda ministoci da shugabannin ma’aikatu za su tattauna akai.

Shugaba Buhari, ya ce, ”Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da ayyuka masu yawan gaske a ƙasar nan musamman na raya ƙasa.

”Mun shimfiɗa sabbin hanyoyi a ƙasar nan masu tsawon kilomita 3,800 sannan kuma mun siyo sabbin jiragen saman yaƙin rundunar sojin saman Nijeriya da za su iso Nijeriya nan ba da daɗewa ba.

”Sannan kuma mun yi wa aƙalla mutum miliyan 38 rigakafin Korona wanda shi ma nasara ce da muka samu.

”Wasu daga cikin manyan nasarorin da aka samu sun haɗa da kammala aikin layin dogo mai tsawon kilomita 326 daga Itakpe-Ajaokuta-Warri da kuma kammala aikin sabunta layin dogo na sama da kilomita 156.5 daga Legas zuwa Ibadan tare da faɗaɗa tashar jirgin ruwa ta Legas, Apapa.

“Akan ayyukan titina, wannan gwamnatin ta gina tituna mai tsawon kilomita 408, da kuma titin SUKUK kilomita 2,499 da kula da titina mai tsawon kilomita 15,961 a faɗin ƙasar nan.

“Wasu daga cikin muhimman ayyukan sun haɗa da gina gadar Neja mai nisan kilomita 1.9 da ta haɗa jihohin Anambra da Delta mai tsawon kilomita 10.30, gyara, ginawa da faɗaɗa titin mota biyu daga Legas zuwa Shagamu-Ibadan, aikin gyaran Abuja-Kaduna–Zaria–Kano, da sauransu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *