Mun fatattaki muggan ɓarayi da ‘yan daba a garin Tafa – Kwamanda Adam Omajudo

Daga MOHAMMED ALI a Tafa

Shugaban Tsaro na Ƙungiyar ‘Neighborhood Watch’ da reshen PCRC ta rundunar ‘yan sanda dake garin Tafa ta Ƙaramar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, Kwamanda Ambasada Adam Omajudo, ya yi iƙirarin cewa, ƙungiyarsa ce ta ‘yan sa kai ta yaƙi wasu muggan ɓatagari da suka addabi al’umma tsawon shekaru, hoɓɓasar da ya ce ta sa aka samu kwanciyar hankali a garin.

Da yake hira da wakilin mu a Tafa Litinin ɗin wannan makon, Kwamanda Adam ya ce, kafin kafa ƙungiyar ta su mai rassa a Chakwama, Dulu, Sisiya, ‘Yan Goro, Dogon Ƙarfe, da Unguwar Gwari baya ga wasu dake Zariya, Kaduna, Jos da kuma cikin wasu ƙananan hukumomi, al’umma sun ɗanɗana kuɗarsu saboda barazanar varayi, ‘yan fashi, ‘yan daba da makamantansu.

Kamar yadda ya ce: “Kafin kafa wannan ƙungiya, al’ummar Tafa sun ga bala’oi iri-iri, musamman muggan ɓarayi da suke fasa gidajen mutane suna yi wa mata fyaɗe, suna sassaran mutane da muggan makamai, sannan su saci abinda suke so, su yi awon gaba, su bar mutane cikin jini, wasu rai hannun Allah.”

Ya ce saboda haka ne, ya jagoranci wasu masu kishi, da goyon bayan ‘yan sandan yankin haɗe da wasu jami’an tsaro, suka kafa ƙungiyar don fuskantar waɗannan masifu da kawo ƙarshen su, yana mai ƙarawa da cewa, bayan abinda ya kira da, “dogon jihadi” akan waɗannan muggan mutane, suka fara samun sauƙi, baya ga kawo ƙarshen daba, da shaye-shaye a tsakanin matasa, da rarrage ƙazamin karuwanci irin ta can baya.

Har gidajen dirama da wasu lungunan shashanci a cikin garin Tafa da kewaye, duk sun karaɗe, kuma sun “share” ilahirin ɓatagarin da suka addabi jama’a a wuraren.

Sai Ambasada Adam ya yi godiya ga DPO na yankin, da tsohon kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna, Ambursa, da ya zama DIG, da Limaman addinin Islama da Kiristoci da duk sauran jami’an tsaron da suka basu goyon baya ɗari bisa ɗari wajen gudanar da aikinsu na tsaro, wanda hakan ya taimaka musu gaya wajen zaƙulo da kuma cafko ɗaruruwan ɓatagari waɗanda suka miqa su ga rundunar ‘yan sanda.

“Alhamdu Lillahi, yanzu mun samu sauƙi, ko ma in ce mun kawo ƙarshen duk ta’addanci a Tafa, tun da hatta ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane mun tava fatattaka, yanzu komai ya yi sauƙi, mutane dai su ci gaba da bamu haɗin kai.”

Sai dai Kwamandan ya yi kukan rashin kayan aiki kamar motar sintiri da makaman fito-na-fito da mugu saboda a cewar shi, “da muna da motocin fatrol da bindigogi kamar yadda ake bawa ƙungiyoyin tsaro irin nasu a wasu jihohin ƙasar nan, da babu inda zai kai Tafa kwanciyar hankali da zaman lafiya. Don haka muna kira ga Maigirma Gwamna Nasir El-Rufa’i da masu kishi da masu hannu da shuni, su kawo mana ɗauki don ƙarin samun ƙwarin gwiwwar tinkara da share duk rashin tsaro daga gari, har ma da makwabta.”

Malam Muhammad Sani Abdullahi da Malam Rilwanu Umar, duk mambobi ne a ƙungiyar da aka kafa tun shekaru shida da suka wuce, kuma mai yawan mambobi sama da 200, sun yaba akan irin kyawun shugabacin shugaban nasu, wanda suka ce, ya samu lambobin yabo a cikin da wajen Nijeriya ba iyaka saboda gaggarumin gudunmawar da ya bayar wajen kawo ƙarshen rashin tsaro a garin Tafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *