Mun gano waɗanda ake zargi da ɗaukar nauyin Boko Haram – Malami

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta gano masu ɗaukar nauyin mayaƙan Boko Haram da suka addabi yankin Arews-maso-gabashin ƙasar.

Babban Lauyan Nijeriya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida a birnin New York a wajen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 76.

Hadimin Malami kan sha’anin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Dr. Umar Jibrilu Gwandu, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Larabar da ta gabata.

Malami ya ce Gwamnatin Tarayya na yin bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da Nijeriya ta ci gaba da kasancewa cikin lumana da bunƙasa. Tare da cewa, za a sanar da ‘yan Nijeriya sakamakon binciken a lokacin da ya dace nan gaba.

Ya ce a halin da ake ciki, bincike ya yi nisa, kuma gwamnati za ta yi bayani kan haka nan gaba. Yana mai cewa, lokacin fasa ƙwan bai yi ba gudun kada a haifar da cikas wa binciken da ake gudanarwa.

Ya ci gaba da cewa, babbar manufar binciken shi ne, don cimma zaman lafiya da tsaro mai inganci a faɗin ƙasa.

A cewarsa, “Mun taki nasarar bankaɗo waɗanda ake zargin su ne ke ɗaukar nauyin mayaƙan Boko Haram, za mu daƙile duka hanyoyin da suke samun kuɗaɗensu sannan mu ci gaba da zurfafa bincike.”

“Wani abu guda da zan shaida muku shi ne, dukkan abin da ya shafi kama mutane da tsarewa, bisa hujjoji na shari’a muka aikata hakan.”