Mun horar da masu ruwa da tsaki kan ilimin dabarun kare kai – DPRC

Daga  MUHAMMAD MUJITABA a Kano

Cibiyar Cigaba da Ayyuka na Musamman da Binkice akan Harkar Ilimi (DPRC), sun shirya bita ta musamman ga masu ruwa da tsaki kan ilimin dabarun kare kai daga matsalar tsaro da garkuwa da mutane a makarantu da maaikatu da sauransu, waɗanda suka futo daga jihar Kano da Jigawa kamar yadda jamii mai bada shawara da dabaru a wannan cibiya Sulaiman Muhammad  ya bayyana a wajen wannan bita wanda aka gabatar a Birnin Kanon Dabo a eanar Alhamis ɗin makon jiya.

Har ila yau ya ce wannan cibiya tana yin wannan ayyuka na wayar da kai akan harkar ilimi, lafiya, da kuma bincike da sauran su, wanda yanzu wannan cibiya ta shirya bita ne akan dabarun kare kai daga matsalar tsaro da ake fuskanta a qasar nan, wanda aka shirya kan masu ruwa da tsaki akan harkar ilimi, da sauran ƙungiyoyin fararen hula waɗanda su ka fito daga Jihar Kano da Jigawa bayan gabatar da irin wannan bita a shekarar da ta gabata a Abuja.

Sulaiman Muhammad ya ƙara da cewa waɗanda aka gayyato a wannan bita sun haɗa da malaman makaranta, ɗaliban makaranta, ma’aikata da shugabannin makarantu a matakai daban-daban wanda suka haɗa da kwamishinonin ilimi ko wakilin su da su ka zo daga Kano da Jigawa, haka kuma akwai sarakunan gargajiya da makamantan su a wannan bita.