Mun kakkaɓe miyagu a dazukan Katagum, cewar magajin Ali Ƙwara

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Ahmad Muhammad Ƙwara ƙani ne ga Marigayi Alhaji Ali ƙwara, kuma uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da marigayin, kuma shine ya gaje shi wajen yaƙi da ‘yan fashi da ɓarayi. A farkon makon da ya gabata ne Ƙungiyar Matasan Arewa ta shirya taron lakca don tunawa da Marigayi Ali Ƙwara kan irin gudunmawar da ya bayar wajen inganta harkokin tsaro, kasuwanci da kuma taimakon al’umma, wanda aka gudanar a garin Azare ta ƙasar Katagum da ke cikin jihar Bauchi. A ƙarshen taron, manema labarai sun tattauna da Ahmad Ƙwara, kamar haka:
 
Me za ka ce kan wannan taro da aka gudanar yau?
Gaskya shi, ɗan’uwana Marigayi Ali Ƙwara lokacin da yake raye, ya yi ayyuka da yawan gaske, kuma ya taimaka wa mutane masu yawa, ya taimaki ɗaukacin al’umma, kuma ya samu goyon bayan jama’a, manya da ƙanana, mace da namiji, don haka waɗanda suka shirya wannan taro sun kyautata mana matuƙa gaya, domin mu suka karrama. shi kam marigayi ya taka tasa rawar, ya tafi ya bar mu da kewa da darussa masu yawa, da muka koya daga gare shi, mu aka karrama domin mu ne muka ga abinda aka yi masa a yau, da fatar addu’o’in da aka gudanar za su isa gare shi. Muna godiya ƙwarai da gaske, Allah ya saka da alkhairan sa, amin.
 
Kai ke jan ragamar gidan ku a yau, kuma kai ke jan sana’ar marigayi mafi wahala, wacce ita ce yaƙi da ‘yan fashi da varayi, shin ina aka kwana?
Alhamdulillahi, tun rasuwar Marigayi Ali Ƙwara, ni ne aka bai wa ragamar yin wannan tafiya, kafin mu fara sai da muka nemi izinin manya a ƙasa kamar shugaban ƙasa, da kuma shi Babban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, mun je mun zauna da shi na kuma samu izinin hukuma na ci gaba daga inda shi ɗan uwana ya tsaya, kuma tun lokacin, cikin shekara guda da rasuwarsa, mun yi ƙoƙari sosai mun yi ayyuka da yawa tare da jami’an tsaron da muke aiki tare da su, kuma an samu nasarori, ba wai anan jihar Bauchi kawai ba , har ma da waɗansu jihohin ƙasar nan, domin mun shiga wasu yankuna a jihohin Kaduna, da Katsina, kuma duka Allah ya ba mu nasarori, don mun kama ɓarayi waɗanda kuma muka miƙa wa hukuma su.

Yaya haɗin kanku da jami’an tsaro?
Gaskiya a wannan batu sai godiya wa Allah domin muna tare da su, ka san shi wannan aiki kamar yadda marigayi yake faɗa muku kullum aiki ne na taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar kama masu aikata laifuka, don haka tare muke da su, sune suke yin aikin su mu dai muna taimaka masu ne kamar yadda a kullum marigayi yake faɗa maku, muna tare da jami’an tsaro, ‘yan sanda da muke aiki da su a ko’ina. Gida da waje, kuma lokacin da muka zauna da babban Sufeto Janar na ‘yan sanda ya ba mu goyon baya sosai, ya ce duk jihar da muka je za mubyi aiki za a qara mana ƙarfin jami’an tsaron da za mu riƙa shiga cikin daji da su, mu yi aikin farautar ɓarayi, idan mu kammala kuma, mu dawo da waɗanda aka haxa mu mu yi aiki da su zuwa gida, ka ga muna aiki da su ba wata matsala mai ɗauke hankali, suna ba mu goyon baya sosai.

Gwamnatocin jihohin da kuke zuwa jihohin su kuke yin aiki, yaya dangantakar ku take da su?
Alhamdu lillahi su ma suna ba mu goyon baya sosai, sun bamu haɗin kai, duk dacewar shi aikin da muke yi akwai sirri a ciki, zabmu iya samun bayanai akan masu laifi, mu shiga gari mu yi aiki mu fito ba wanda ya sani. Sai dai bayan mun kammala, kuma wani lokaci kamar yadda wasu gwamnatocin jihohi ke neman gudunmawar sa, lokacin yana raye, domin a yaƙi ‘yan fashi da makami. Muna samun haɗin kai kan haka, ka san muna amfani da waɗanda suke babmu bayanai kan maɓoyar ɓarayi, wani lokaci su ma ɓarayin kamar sace muke yi masu, ko mu yi masu kwanton-ɓauna, mu ritsa su mu kame su. Shi ya sa sai mu shiga jihohi mu yi masu aiki mu fita, jama’a ba su sani ba.

A baya, shi marigayi ya kan yi wata dabara, in ya kama ɓarawo sai ya yi amfani dan shi ya kira sauran ‘yan ƙungiyar su a kama su baki ɗaya, ko kuma kuna yin haka?
Gaskiya, muna yi kuma ka san kafin Ali Ƙwara ya rasu, ya bar masu bayar da bayanai kan maɓoyar ɓarayi, waɗanda muke kira (informants) a jihohi masu yawa, waɗanda a da su ɓarayi ne, sun bar sata sun koma suna baibwa Ali labarai, waɗannan mutane har yanzu muna tare da su, muna zaune da su bayan rasuwarsa. Na shaida masu cewar, Ali Ƙwara ya tafi amma ya dawo, saboda haka aikin da a da yake yi da ku mu cigaba, duk inda suka ji wani labari mai kyau sukan bamu bayanai, mu kuma mukan je mu yi abinda ya kamata, yanda yake yin tsarin sa da dabarun sa, haka muke yi.

A yau Nijeriya ta Arewa na fama da matsalar fashi da makami, da gungun ɓarayi masu sata, da garkuwa da mutane da suke zaune cikin dazuzzukan mu, ko akwai wani yunƙuri na shiga cikin dazuzzukan domin yaƙi da ɓarayin?
Gaskiya, muna kazar-kazar sosai, musamman a yankunan mu na ƙasar Katagum, ba wanda zai ce maka akwai wani mai sata da garkuwa da mutane, ko gungun su a cikin dazuzzukan mu, munbyi yaƙi da su kuma Allah ya taimake mu mun kore su daga ciki, kasan anbce kyawun kyautata wa mutum ya fara daga gida, don haka daga gida na fara, kuma mun fita, domin yanzu haka, zancen da nake yi maka, muna kan gudanar da ayyuka a cikin dazuzzukan jihar Katsina, kuma muna iya ƙoƙarin mu a cikin jihar. Daga nan kuma za mu tinkari jihar Zamfara da ikon Allah.

Amma har yanzu akwai dajin Ƙasar Lame Burra a nan cikin jihar Bauchi, shi ma ana koken cewar, baƙin miyagun ɓarayi suna ɓoye a cikin dajin, ko ka taɓa kai samame wurin?
Gaskiya ba mu shiga cikin wancan daji ba , amma cikin makon da ya gabata mun yi magana akan wannan daji na Lame Burra da jami’an gwamnatin jiha. Kuma za mu shirya masa domin mu bayar da gudunmawar na yadda a tsarkake dajin cikin ikon Allah. 

Ko mutum nawa kuka kama tunda kuka fara farmaki?
Gaskiya, mun kama da yawa, a ƙaramin lissafi mun kama ɓarayin fiye da 50, kuma kasan kamar yadda marigayi yake yi, idan mun kama varawo muka tatse bayanan sa, sai mu bar wa jami’an ‘yan sanda domin su kai shi ya fuskanci hukunci kan laifuffukan da ya aikata.
 
Shi Marigayi ya sha kokawar cewa, zai kama ɓarawo amma sai xan sanda ko kotu ta sake shi, ko kai ma ka samu irin wannan matsala?
A yanzu dai, ni ban samu irin wannan matsala ba, muna samun goyon baya sosai, domin duk waɗanda muka kama, in dai mu muka ba su sukan yi masu hukunci, jam’ian ‘yan sanda da na kotuna duk suna ba mu goyon baya, saboda duk cikin waɗanda na kama babu wani a waje duk suna tsare a gidan gyara halin ka.

Wacce shawara za ka bai wa jama’a?
A gaskiya, ba abinda mu ke nema a wurin jama’a kamar goyon baya da haɗin kai, haɗi da addu’o’i daga ɗaukacin jama’a. Muna buƙatar addu’o’i ƙwarai da gaske a wurin jama’a, su kuma ɓarayi muna shawartar su, su tuba su daina waɗannan ayyuka na zalunci, su koma kan sahihiyar hanya ta rayuwa, domin abubuwan da suke aikatawa ba su da kyau. Masu magana sun ce, rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya, saboda haka, ko su tuba, ko wata rana Allah zai ba mu nasara a kan su, a kama su a hukunta su da ikon Allah.