Mun kama ɗan sanda bogi, ɗan jarida da malamin addini bisa afka wa gidan alƙali – ’Yan Sanda

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar `yan sandan Nijeriya ta yi nasarar kama wasu mutane 14 da ake zargi da shiga gidan Mai Shari’a Mary Odili kwanakin baya. Daga cikin waɗanda ake zargin har da wani ɗan sandan bogi mai suna Lawrence Ajodo da wani ɗan jarida da kuma malamin addinin Musulunci.

Da ya ke gabatar da mutanen ga manema labarai a Abuja jiya Alhamis, Kakakin ‘Yan Sanda na Ƙasa, Mista Frank Mba, ya ce, an kama mutanen ne bayan ƙaddamar da bincike.

“Har yanzu akwai aƙalla mutum 10 da ‘yan sanda ke alaƙantawa da lamarin da suka tsere,” in ji Mista Mba.

Wasu mutane ɗauke da makamai sun kutsa kai gidan alƙaliyar ta Kotun Ƙoli ranar 29 ga watan Oktoba a Unguwar Maitama da ke Abuja, Babban Birnin Nijeriya.

Tun a lokacin rundunar ‘yan sandan ta musanta cewa jami’anta ne suka shiga gidan tare da bayyana aniyar ƙaddamar da bincike.