Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano, mai wakiltar ƙananan hukumomin Ƙunchi da Tsanyawa kuma shugaban kwamitin ayyuka da raya birane a majalisa, Hon.Garba Ya’u Gwarmai ya ce yana mutuƙar alfahari da irin ƙudurorin da yake gabatarwa a matsayinsa na ɗan majalisa don kyautata cigaban al’ummarsa da Jihar Kano bakiɗaya.
Ɗan majalisar ya bayyana haka ne yayin da yake hira da manema labarai, inda ya ce cikin kudurorin da ya gabatar sun haɗa da na neman a bai wa ma’aikata kuɗin rago a zamanin gwamnatin Injiniya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, duk da hakan bai tabbata ba.
Ya kuma yi ƙoƙarin a sauya manhajar ilimi tun daga makarantar firamare da na sakandire har jami’oi a riƙa karatu da harshen Hausa, duba da yadda a ƙasashe da dama da suka samu cigaban ilimi a duniya na amfani ne da harshensu na uwa irinsu Chana, Iran da Jamus da sauran ƙasashe.
Ya yi nuni da cewa in har za a iya samun ɗalibi ya samu babban sakamako da harshen da ba nasa ba, to idan aka koya masa da yaren shi za a samu cigaba mai yawa, da an yi amfani da ƙudurin da za a samu cigaba mai yawa a Kano.
Hon. Garba Ya’u ya ce karɓuwa da yake da ita a siyasa a yankin mazaɓunsa na samuwa ne saboda tun lokacin da ya yi kansila na lafiya da na walwala da na ayyuka a Ƙaramar Hukumar Ƙunchi ya yi amfani da dama wajen kyautatawa mutane.
Ya ƙara da cewa tunda aka kafa Ƙaramar Hukumar Ƙunchi da Tsanyawa ba a samu wani ɗan majalisar jiha da ya bada gudunmuwa kamar yadda ya bayar ba, don a halin yanzu ya yi rijiyar burtsatse sama da 600 da masallatai 30.
Ya cigaba da zayyana cewa, ya gina makarantu sama da 100, banda kayan more rayuwa a Ƙunchi da Tsanyawa.
A cewarsa, babu wanda yake taimaka wa ɗimbin al’umma kamar shi, inda ya ce ya raba wa mutanensa motoci da babura da kekunan hawa da na ɗinki da siminti da kwanon rufi da sauran kayayyaki.
Hon. Garba Ya’u Gwarmai ya ce, “a dukkan harkar rayuwa, ba siyasa kaɗai ba, ba a iyawa ɗan Adam, don kamalarsa bata da iyaka, kuma abinda yake faruwa a siyasa a halin yanzu ba baƙo ba ne, dama idan kakar zaɓe ta zo za a ga wasu na sauya sheka don neman biyan buƙatar su, daga wannan jam’iyyar zuwa waccan, kowane ɓangare ana samun hakan amma su a APC wannan baya basu tsoro ko ya rage musu tasiri, wanda kuma suke fita daga APC zuwa wata jam’iyyar yawanci ko akwatinsu basa iya kawowa a zaɓe, amma akwai mutanen arziƙi a ciki da suka fita, kuma suna jin ciwon hakan, amma mafi yawanci tarkace ne da ba za su iya wani abu ba kuma za a gani lokacin zaɓe.”
Ɗan majalisar mai wakiltar Ƙunchi da Tsanyawa ya yaba wa Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibrin da ɗan majalisar Tarayya Sani Bala wanda suke aiki tare da su a matsayinsa na ɗan majalisar jiha don ganin an samu nasara a ƙoƙarin ganin an sauya wa garin Ƙuncin suna, wanda sai an tura jihohi 36 an samu amincewa ta kaso biyu bisa uku sannan a samu tabbatar hakan, sunyi magana da yan majalisu na jahohi 36 sun nuna amincewa da goyon bayansu in Allah ya so Ƙaramar Hukumar Ƙunchi za ta sauya suna zuwa Ƙaramar Hukumar Gari kusan abinda ake jira lokaci ya yi a tura kuma wannan buƙata za ta biya da yardar Allah.
Hon. Garba Ya’u ya bayyana cewa, kasancewarsa ɗan majalisa kusan shekaru 12, abinda ya fi alfahari da shi a ayyukan da yake yi shi ne samar da ruwan sha.