Mun samu masu sa jari a Nijeriya daga ƙasashen BRICS – Shettima

Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa Najeriya ta samu kuɗaɗen zuba jari daga waje har Dalar Amurka biliyan 1.27 daga ƙasashen BRICS zuwa watan Juni 2024. Wannan ya nuna ƙaruwar kuɗaɗen da aka samu idan aka kwatanta da Dalar Amurka miliyan 438.72 da aka samu a irin wannan lokaci a shekarar 2023. Ƙasashen BRICS sun haɗa da Brazil, Rasha, Indiya, Sin, da Afirka ta Kudu, tare da sabbin mambobi kamar Iran, Masar, Habasha, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

A lokacin taron China-Africa Inter-Bank Association Forum da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, Shettima wanda ya samu wakilcin mai ba shugaban ƙasa shawara ta musamman, Dakta Aliyu Modibbo, ya yi tsokaci kan kyakkyawar alaƙar tattalin arziki dake tsakanin Najeriya da ƙasashen BRICS.

Ya ce Nijeriya a matsayin ƙasa mai haɗin gwiwa ya nuna yadda ƙasar ke himmatuwa wajen gina dabarun haɗin kai domin samun ci gaba na cikin gida.

Shettima ya bayyana cewa, “Nijeriya ta kasance ƙasa mai buɗe hanya ga haɗin gwiwa da ke tallafawa burin ci gaban mu. Wannan ya bayyana matsayin mu a taron BRICS da aka gudanar a Afirka ta Kudu bara, da kuma gasar BRICS na watan Oktoba 2024 a Rasha. Samun Dalar Amurka biliyan 1.27 daga ƙasashen BRICS zuwa watan Yuni 2024 ya nuna ƙaruwar amintar juna a tsakanin mu da ƙasashen.”

Ya kuma jaddada cewa Sin ce ta fi kowacce ƙasa hulɗa da Nijeriya a fannin ciniki, inda jimillar cinikayya tsakanin ƙasashen biyu ta kai Naira tiriliyan 7.38 a farkon rabin shekarar 2024.

Mataimakin shugaban ƙasa ya danganta wannan ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyyar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya rattaba hannu kan muhimman yarjeniyoyi guda biyar a yayin ziyarar sa ta aiki zuwa kasar Sin a watan Satumba 2024.

Waɗannan yarjeniyoyi sun haɗa da shirin “Belt and Road Initiative” wanda ke da nufin inganta ci gaban ababen more rayuwa a Nijeriya. Shettima ya ƙara da cewa, “Alaka mai zurfi da Sin ta fuskar tsarin kuɗi da na banki na da muhimmanci wajen tabbatar da haɗin kai mai ɗorewa tsakanin ƙasashen mu.”