Mun san inda ɗaliban Islamiyya 136 da aka yi garkuwa da su suke, cewar Gwamnatin Neja

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa a haƙiƙanin gaskiya ta san inda ɓarayin da kuma ɗaliban Islamiyya 136 da aka yi garkuwa da su daga Makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da Tegina a Ƙaramar Hukumar Rafi suke.

Sai dai, gwamnatin ta ce babbar damuwarta ita ce gudun lalacewar lamunin da zai taimaka wajen ceto ɗaliban.

Waɗannan bayanai sun fito ne daga bakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Ibrahim Matane a Minna, babban birnin jihar.

Idan dai ba a manta ba, a baya gwamnatin jihar ta sha faɗar cewa ba za ta biya kuɗin fansa ga ‘yan bindiga ko ‘yan fashin daji a jihar ba.

Matane ya ce iyayen yara sun roƙi gwamnatin jihar sau da dama kan kada ta yi amfani da matakan da ta shirya ɗauka gudun kada a samu hasarar rayuka a cikin yaran.

Manhaja ta fahimci cewa ‘yan fashin dajin sun ɓoye yaran a wurare daban-daban da ba a sani ba har guda 25 ya zuwa lokacin da za a ƙarasa biyan su Naira milyan 4.6 da babura guda biyar.

Binciken Manahaja ya gano cewa, iyayen yaran da hakumar makarantar suna ta faɗi-tashin ganin sun tara Naira milyan 3 don sayen babura kamar yadda ‘yan fashin suka buƙata don kuɓutar da yaran.

Sama da kwanaki 60 kenan da ‘yan fashin dajin suka yi garkuwa da waɗannan yara wanda har yanzu ana kan neman yadda za a yi a ceto su lami lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *