Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ce tun hawansa mulki gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin kawo tsarin toshe duk wasu kofofin da kuɗaɗen gwamnati ke sulalewa a jihar.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a wajen taron bitar da Gidauniyar Jihar Katsina ta shirya na shekarar 2023 da ya gudana a gidan gwamnatin jihar Katsina.
Raɗɗa ya kuma ce gwamnatinsa ta kuma ɓullo da tsare-tsare masu inganci da za ta tunkari matsaloli da ƙalubalen da jihar ke fuskanta musamman a sha’anin tsaro, aikin gona, zaman kashe wando a tsakanin matasa da sauransu.
Ya bayyana Gidauniyar jihar Katsina da cewa, ta tallafa sosai wajen kawo cigaba a jihar da kuma mara baya ga tsare-tsare da kudurorin gwamnati na sauƙaƙa wa al’umma a harkokin yau da kullum.
Da yake jawabi a wajen taron, tsohon shugaban Nijeriya kuma shugaban Gidauniyar na farko, Muhammad Buhari, ya ce kwamitin amintattu haɗin guiwa da majalisar mashawartan Gidauniyar ne suka shirya taron bitar domin zaƙulo sabbin fasahohin da za su ƙara haɓaka ayyukan Gidauniyar.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce amfanin wannan Gidauniya ba zai misaltu ba a jihar Katsina, ganin yadda ta ba da gudunmuwa wajen inganta tsaro da haɗin kan al’umma.
Kazalika, ya ce irin cigaban da Gidauniyar jihar Katsina ta kawo ga al’ummar jihar abin a yaba ne, kan haka ne ya yaba da irin hangen nesan kwamitin amintattu na Gidauniyar da ya shirya wannan taron.
Shugaban Gidauniyar jihar Katsina, Dr Umar Mutallab ya yi kira da a ba matasa dama domin su ba da tasu gudummuwa a cikin ayyukan Gidauniya domin ayyukanta su ɗore.
Daga nan, ya yaba da yadda Gidauniyar jihar Katsina ta farfaɗo da kwamitin amintattu da take da shi da majalisar masu ba da shawara domin jihar Katsina ta cigaba da amfana da ayyukan Gidauniyar.