Mun zo aikin ceto ne, cewar Zaɓaɓɓen Gwamnan Zamfara

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a’ya ƙaddamar da kwamitin karɓar mulki a ranar Talata a Gusau, babban birnin jihar.

Yayin ƙaddamar da kwamitin mai membobi 60, Dauda Lawal ya jaddada cewa ya zo aikin ceto ne tare da sake gina Jihar Zamfara.

Sanarwar da ofishin zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar mai ɗauke da sa hannun Sulaiman Bala Idris ta nunar cewa, an kafa kwamitin karɓar mulkin ne a ƙarƙashin jagorancin tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda, M.D Abubakar.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da kwamitin, mai girma Dauda Lawal, ya ce nauyin da ya rataya a kan kwamitin shi ne gudanar da shirye-shiryen da suka dace domin karɓar mulki cikin kwanciyar hankali a Jihar Zamfara.

Ya bayyana kwamitin a matsayin taron ƙwararru da ke da gogewar shekaru a ɓangarori daban-daban, waɗanda aka zaɓo su cikin tsanaki domin shiga cikin tsarin karɓar mulkin.

“Canjin da al’ummar Zamfara suka zaɓa, canji ne daga rashin tsaro, rayuwar talauci, zuwa rayuwa ta tsaro, wadata da walwala, riƙon amana, da mutunta doka.

“Kwamitin amsar mulkin mai membobi 60 an kafa shi ne da nufin fara dukkanin shirye-shiryen da ya kamata tare da tsara yadda za a samu sauyi cikin sauƙi na sabuwar gwamnatinmu a jihar wadda za ta fara aiki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

“An ɗora wa kwamitin alhakin samar da ingantaccen tsarin haɗin gwiwa da samar da hanyar sadarwa ta yau da kullum da Gwamnati mai barin gado tare da karɓar ragamar gudanarwar gwamnati mai zuwa domin samun nasarar karɓar mulkin.

“Kwamitin zai kuma haɗa hannu da ma’aikatu, rassa da kuma hukumomi, sannan zai duba kuɗaɗen gwamnati mai barin gado tare da maida hankali kan rasiɗai, ƙadarori, lamuni da sauransu.

“Al’ummar jihar Zamfara na da kyakkyawan fata; sun zaɓe mu ne cike da imanin za mu iya ceto tare da sake gina jiharmu.

“Mun kuma zaɓe ku a matsayin membobin kwamitin karɓar mulki saboda mun yi imanin cewa tsawon shekarun gogewarku da ƙwarewarku, za mu iya aza harsashi ga gwamnati mai jiran gado domin ta yi nasara kan aikin ceton da ta sa gaba.

“Da wannan taƙaitaccen bayani da kuma yardar Allah, a halin yanzu, nake ƙaddamar da wannan kwamitin na karɓar mulki,” in ji Dauda Lawan