Za mu iya tattara sakamakon zaɓe ta amfani da fasahar zamani – INEC

Daga WAKILINMU

Duk da ra’ayin da wasu ‘yan majalisun tarayya suka yi kan cewa batun tattara sakamakon zaɓe ta hanyar amfani da fasahar zamani abu ne da ba zai yiwu ba saboda rashin hali ta ɓangaren Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) da kuma rashin wadatar netiwoki a wasu sassan ƙasa, sai ga shi Asabar da ta gabata aka ji INCE ɗin ta fito ta bayyana cewa lallai tana da halin da za ta attaro sakamakon zaɓe daga sassan ƙasa baki ɗaya ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Tun farko, sai da ‘yan majalisun tarayya suka tafka zazzafar muhawara kan wannan batu na yiwuwar yin amfani da fasahar zamani wajen tattarowa da kuma miƙa sakamakon zaɓe, wanda har ya kai ga an samu hayaniya a majalisar.

Lamarin da ya sanya a Alhamis ta makon jiya ‘yan Majalisar Wakilai suka ƙalailaice sahe na 52(2) na dokokin zaɓe wanda ke magana a kan tattara sakamakon zaɓe ta hanyar amfani da na’ura.

A nasu ɓangaren, sanatocin Nijeriya sun mayar da hankali ne kan dokar da ta tilasta wa INEC neman izini daga wajen Hukumar Sadarwa ta Ƙasa da Majalisar Tarayya kafin ta soma amfani da hanyar kaɗa ƙuri’a ta amfani da fasahar zamani a sassan ƙasa.

A cewa ‘yan Majalisar Wakilan da ba su goyi bayan yin amfani da fasahar zamanin wajen tattara sakamakon zaɓe ba, wai wasu sassan Nijeriya ba su da netiwokin da ake buƙata a yankunansu wajen aiwatar da tsarin.

Yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels a Asabar da ta gabata, Shugaban Shirin Wayar da Kan Masu Zaɓe na Ƙasa na INEC, Mr Festus Okoye, ya ce matsayin INEC a bayyane yake.

Saboda a cewarsa a baya sun kwatatnta aiki da fasahar zamani kuma an ga yadda suka tattaro sakamakon zaɓe daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Don haka jami’in ya ce, “Matsayinmu a bayyane yake, muna da halin yin haka kuma muna da niyyar zurfafawa wajen amfani da fasahar zamani a harkokin zaɓe.

“Sai dai kundin tsarin mulki da kuma doka su ke ba mu ƙarfin da muke aiki da shi, za mu ci gaba da yin amfani da ƙarfin da doka da kundin tsarin mulki suka bai wa hukumar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *