Muna da katin zaɓe 389,000 da ba a karɓa ba a jihar Kano — INEC

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Hukumar Zaɓe Mai zaman kanta ta Ƙasa, INEC ta ce akwai sama da katikan zaɓe dubu ɗari uku da tamanin da tara da masu su ba su je sun karɓa ba a jihar Kano.

Kwamishinan zaɓe na jihar, Riskuwa Shehu ne ya bayyana haka lokacin da Kwamishinan Tarayya na Hukumar Ƙorafe-ƙorafe, Ahmad Daɗinkowa ya kai masa ziyara a jiya Alhamis.

Riskuwa, wanda ya samu wakilcin Sakataren Gudanarwa, Garba Lawan ya ce katikan da ba a karɓa ɗin be tun na shekarun 2011 zuwa 2018 ne.

Ya ce mutane ba sa son zuwa su karɓi katin zaɓen su.

Sannan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su zage dantse wajen wayar da kan al’umma don su rika zuwa su na karɓar katikan su na zaɓe kafin babban zaɓe mai zuwa,

Ya kara da cewa a aikin rijistar da aka kammala da karfe 12 na daren ranar Lahadin da ta gabata, an yi wa sabbin masu zaɓe 569,103 a jihar ta Kano.