Muna da kyakkyawar fata Atiku Abubakar zai nasarar zama Shugaban Ƙasa a kotu – Mai-Nasiha

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Wani ɗan Jam’iyyar PDP a Jihar Kano, Alhaji Salman Mai Nasiha ya bayyana cewa a yadda suke ganin ana gudanar da shari’ar ƙorafin zaven Shugaban Ƙasa a Babbar Kotun Abuja, suna kyautata zaton Atiku Abubakar zai yi nasara.

Mai-Nasiha ya bayyana hakan ne yayin da yake hira da ‘yan jarida, inda kuma ya yi nuni da cewa al’ummar ƙasar nan sun yi wa Buhari kyakkyawan zato a mulkinsa za su samu saulin rayuwa da walwala amma sai ga shi ya jefa mutane a mafi ƙuncin rayuwa da ba a tava tsammani ba.

Ya ƙara da cewa yanzu ga shi yana shirin barin mulki amma yana cigaba da ƙoƙari na ciwo bashi da zai lafta wa ƙasar nan ya daɗa tunkuɗa ‘ya’ya da jikoki a cikin mawuyacin yanayi saboda ɗimbin bashi da ya karvo ya laftawa lasar.

Mai-Nasiha ya ce daga irin furuci da Shugaba Buhari da Shugaban Hukumar Zave na Ƙasa Mahmoud Yaƙubu suka riƙa yi sun zaci za a gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar nan a 2023, amma sai aka yi zaɓe mai cike da maguɗi da hakan ya sa ɗan takararsu na shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya garzaya kotu domin ƙalubatantar zaɓen shugaban ƙasa da aka bayyana Tunubu a matsayin wanda ya yi nasara.

Mai-Nasiha yace daga yadda aka soma zaman sauraron kotun ƙarar zaɓen suna da fatan za a tabbatar wa Atiku Abubakar nasara ya zama shugaban ƙasa.

Ya ce Jam’iyyar PDP kowa ya san tana da kyawawan manufofi da ta wanzar a mulkinta aka samu cigaba sosai.

Amma mutane na nadamar bai wa APC dama ta mulkin ƙasar nan duk abinda suke tsammani na kawo sauyi ya gagara.

Salman Mai-Nasiha ya yi nuni da cewa ko yanzu babu gami tsakanin gwamnonin PDP dana sauran jam’iyyu a manufofi na cigaba shi ya sa ma jama’a suka sake zaɓar gwamnonin Taraba, Bauchi, Adamawa domin gamsuwa da yadda suke gudanar da mulki.

Haka ma a Zamfara sun zavi PDP sakamakon rashin gamsuwa da gwamnan APC da yake kai.