Muna dab da warware matsalar da ɗaliban Kano a Cyprus ke fama da su – Abba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Kano, injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin tabbatar da cewa ɗaliban Kano da ke karatu a Cyprus sun sami shaidar kammala karatunsu.

Wannan na ƙunshe ne cikin wani jawabi da ya fitar ta bakin Sunusi Dawakin-Tofa, darakta-janar na yaɗa labaran gwamnan Kano a ranar Litinin.

Ya ce gwamnan a yanzu haka yana ƙasar ta Cyprus domin magance matsalar da ɗaliban suka daɗe suna fama da su.

ɗaliban dai sun kasa karɓar shaidar karatunsu ne saboda rashin biyan kuɗin makaranta da gwamnatin da ta gabata a jihar Kano ta yi.

“Abba ya yi taro da mahukuntan makarantar da ke jami’ar Near East domin tattauna yadda za a kai ga sakin shaidar karatun ɗaliban da suka kammala karatu a tsakanin 2015 zuwa 2019.

“Da yawa daga cikin waɗanda suka kammala karatun sun karanta harkar lafiya ne da karatun jinya waɗanda suka gaza cika burinsu saboda kasa biya musu karatu da aka yi.”

Dawakin-Tofa ya ce, gwamnan ya bayyana halin da suka shiga a matsayin koma baya ga ɗaliban da kuma jihar.

Ya kuma jaddada buƙatar samun ƙwararru a ɓangaren lafiya kuma gwamnan ya ce an samu nasara a tattaunawar da ake yi inda ya tabbatar da cewa za a warware matsalar.

“Da zarar an warware wannan matsalar, ɗaliban za su samu damar cika burinsu da kuma ba da gudunmowarsu ga cigaban jihar Kano,” a cewarsa.