Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban Jam’iyyar NNPP na ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Sulaiman Muhammad Chamba ya bayyana cewa sun yi matuƙar farin cikin da zaɓen Shugaban ƙaramar Hukumar Fagge da kansilolin da ya gudanar Asabar ɗin da ta gabata a Kano.
Sulaiman Chamba ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin rantsar da mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Fagge da zaɓɓaɓɓun kansilolin yankin da aka zaɓa.
Ya ce suna yi wa jama’a da suka taimaka wajen samun wannan nasara su kuma waɗanda Allah ya bai wa nasara na muƙamai Allah ya ba su dama da ikon aiwatar da nauyi da Allah ya ɗora musu da al’umma suka zaɓe su akai musamman ma kada su manta da rantsuwa da suka yi na riƙe amana.
Shugaban jam’iyyar na NNPP na ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Sulaiman Muhammad Chamba ya yi nuni da cewa ko a zaɓe da aka yi a baya ba wani rigima da aka yi a Fagge wannan alama ce da ta nuna koyaushe al’umma a ƙaramar hukumar Fagge suna zaune lafiya ana kuma biyayya ga juna domin mutanen kansu ya waye a siyasance.
Hon Sulaiman Muhammad Chamba ya yi kira ga sabbin shugabannin ƙaramar hukumar da cewa duk wanda aka damƙawa amana ya kamata ya tuna baya, domin an yi shugabanni da kansiloli da suka gabata sun zama tarihi don haka abinda ka shuka shi za ka girba kowa ya tuna cewa abinda ya faru a baya na rashin kirki akan wasu karya faru a kansa, domin dukiya ko kuma mulki da Allah ya baka nasa ne, ya baka ne domin ka kyautatawa mutane.