Muna Nazarin Matakan da za mu Dauka akan Mbarika – Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce, tana nan tana nazarin irin matakin da zata dauka, malamin jamiar nan da ke East Carolina a kasar Amurka.

A farkon makon nan ne dai, mai magana da yawun gwamnatin jihar, ya shelanta cewa, wannan jami’a ta dauki gwamna Ganduje aiki a matakin farfesa, saboda kwarewarsa a fannin mulki da jagoranci nagari.

Amma yan kwanaki bayan wannan shela, sai ga jami’ar ta fito, ta karyata wannan batu na daukar aiki.

Wani mai magana da yawun gwamnatin, malam Salihu Tanko Yakasai yace, “muna nan muna nazarin matakin da ya kamata gwamnati ta dauka akan wannan malamin jami’a. domin dai mu ba mu muka nema ba. Kuma gwamna Ganduje ya zama gwamnan Kano ne, da digirin mastas biyu da kuma digirin digirgir, in da ace akwai abinda ya fi Farfesa ma, ya cancanci a bashi”

Mai magana da yawun gwamnatin, ya yi wannan bayanin ne a wani shiri na gidan radiyon Freedom, da ake kira “mu tattauna”. Ya kara da cewa “ya zama wajibi hukumar jami’ar ta dau matakin ladabtarwa akan wannan malami, domin shaidu sun nuna dai, ma’aikaci ne a jami’ar. Ta yaya ya rubuta wasika da hatimin jami’ar, kuma ta yaya ya saka bayanin daukar aikin a shafin jami’ar na intanet?” in ji shi malam Salihu Tanko Yakasai.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*