Muna neman ƙarin kuɗi don magance matsalar marasa zuwa makaranta, inji Ministan Ilimi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan ilimi, Olatunji Alausa, ya yi kira da a ƙara wa yawan kuɗin da ake bai wa ɓangaren ilimi domin magance matsalar almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.

Mista Alausa ya yi wannan kira ne a ranar Talata a Abuha a yayin da yake kare kasafin kuɗin ma’aikatar ilimi na 2025 a gaban kwamitin kula da manyan makarantu da TETFund da ilimi na majalisun ƙasar nan.

Kalmar al’amajiri dai ta samo asali ne daga harshen Larabci ‘Al-Muhaajirun’ wanda ke nufin ‘masu hijira’.

A rahotan da UNICEF ta fitar, ta ce, akwai yara almajirai kusan miliyan 9.5 da adadin yaran da ba sa zuwa makaranta da ya kai kaso miliyan 18.3, wato a duk yara uku, ɗaya ba ya zuwa makaranta a ƙididdigar asusun.

Sai dai mafi yawan almajirai na Arewacin Nijeriya ne. Kuma a zamanin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya yi ƙoƙarin gina makarantu domin bai wa almajirai damar zuwa makaranta.

Amma gwamnatocin da suka biyo bayansa, sun gaza kula da su.

A yayin kare kasafin kuɗin, Alausa ya bayyana damuwarsa kan yadda ake cigaba da samun ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta.

“Kuɗin da ake bai wa hukumar kula da almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta ba kai ya kawo ba. Muna buƙatar ƙari,” a cewar ministan.

Mista Alausa ya ce, kusan da yawan makarantun almajirai ba sa aiki cikin sama da guda 100 da ake da su a Arewacin Nijeriya.

Ya koka kan yadda aka yi watsi da tsarin amma ya bai wa shugaban ƙasa Bola Tinubu tabbacin cewa zai farfaɗo da waɗannan makarantu na almajirai.

“Tabbas, cikin makarantu sama da 100 da ake da su, ‘yan kaɗan ne suke aiki,” a cewarsa.

Daga nan ya nuna buƙatar zuba jari a wajen bunƙasa rayuwar bil’adama inda ya ce ƙarancin ayyukan gina ɗan’adam na barazana ga cigaban ƙasar nan.

Mista Alausa ya ce gwamnatin tarayya na cigaba da ninka ƙoƙarinta wajen ganin ta magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta ta hanyar aiki da gwamnatocin jihohi domin nemo mafita.

“Don haka, muna aiki tare da su. Wannan abu ne da yake buƙatar neman haɗin guiwa. Adadin yaran da ba sa zuwa makaranta abin damuwa ne. Wannan abu ne da ya shafi yanki ɗaya, abu ne da ya shafi ko’ina.”

“Akwai buƙatar mu fuskanci wannan matsala, in ba haka ba, matsalar nan ba za ta daina bibiyarmu ba. Wannan ta sa muka yi wani zama da gwamnonin Nijeriya domin duba ta yaya za mu haɗa guiwa. Muna aiki da da dukkan kwamishinonin ilimi 36 da suke ƙasar har da na birnin tarayya Abuja.”

A yayin da yake magana, shugaban kwamitin manyan makarantu da asusun TETFunda, Muntari Dandutse, ya amince da buƙatar haɗin guiwa a tsakanin gwamnatocin tare da nuna buƙatar ƙarin kuɗin da ake bai wa ma’aikatar ilimin domin cike giɓin da ake da shi a ɓangaren ilimi a Nijeriya.

“A matsayinmu na ‘yan majalisa, muna da wani nauyi da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ɗora mana na dabbatar an kasafta arziƙin ƙasa yadda ya kamata ga kowanne ɓangare.”