Muna son matasa su karkato da tunaninsu ga sana’o’in gargajiya, Inji Sarkin Askan Jos

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A yayin da sana’o’in gargajiya daban-daban ke samun koma baya, saboda sauye sauyen zamani da rashin samun tallafin hukumomi. An fara ganin farfaɗowar wasu tsofaffin sana’o’in Hausawa na iyaye da kakanni da ke ƙoƙarin jawo hankalin matasa ga raya al’adunsu na gado, don samun abin dogaro. Harkar wanzanci na daga cikin waɗannan sana’o’in da daruruwan matasa ke cin abinci a cikinta, sakamakon sabbin jinin shugabanni da aka samu da ke ƙoƙarin inganta sana’ar da kuma qara kusantar da ƙungiyar raya harkar wanzanci ga gwamnati, don kawo wa sana’ar cigaba. Wakilin Blueprint Manhaja a Jos, ABBA ABUBAKAR YAKUBU ya gana da Sarkin Askan Jihar Filato, masanin shari’a, kuma ƙwararren mai aikin shiga tsakani da sasanta saɓani, Ishaq Danjuma Sarki, domin jin yadda suke ƙoƙarin bunƙasa harkar wanzanci a Jihar Filato.

MANHAJA: Yallaɓai, muna son ka gabatar mana da kanka.

Assalamu Alaikum, da farko dai sunana Ishaq Danjuma, Sarkin Askan Jihar Filato. Ɗan Amar ɗin Wanzaman Arewa, kuma Shugaban Ƙungiyar Haɗin Kan Wanzaman Jihar Filato, har wa yau kuma ni ne Muƙaddashin Babban Sakataren haɗaɗɗaɗiyar Ƙungiyar Wanzaman Gargajiya ta ƙasa. Har wa yau ni ne Muƙaddashin Babban Sakataren Ƙungiyar Wanzamai ta Afirka ta Yamma. Sannan kuma bayan kasancewa ta Alƙali a kotun Majistire ƙarƙashin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Filato, ina kuma cikin wata ƙungiya ta Ƙwararrun Lauyoyi da Alƙalai Masu Shiga Tsakani da Sasanta Al’umma. Hidimar dai da ake yi tana da yawa gaskiya. Sai dai Allah ya dafa mana.

Ko za ka gaya mana manufofi da ayyukan wannan jungiya?

Manufar kafa wannan ƙungiya shi ne a haɗa kan wanzaman mu na gargajiya, domin aiki tare ta yadda za a bunƙasa wannan sana’a da samar mata da hanyoyin cigaba na zamani, da kuma haɗa gwiwa da hukumomi da gwamnati yadda za a samu tallafi da shigar da mu cikin wasu tsare-tsare na ayyukan kiwon lafiya, ƙarƙashin irin tsarin da muka gada na iyaye da kakanni.

Kawo yanzu waɗanne sabbin abubuwa ne za ka ce wannan ƙungiya taku ta ɓullo da shi na cigaba?

Babu shakka akwai wasu sababbin abubuwa da za muka kawo su, kamar misalin mun yi ƙoƙarin daƙile matsalar zaman banza a tsakanin matasa, ta yadda ƙungiyarmu ta ɗauki nauyin koya wa matasa sana’ar aski na zamani da ake yi da na’urar yin aski mai amfani da wutar lantarki, inda yanzu matasa da dama suna da shagunan da suka kama kuma suke gudanar da wannan sana’a yanzu haka.

Sannan akwai sabuwar hanyar yin ƙaho ta zamani da muka ɓullo da ita ta hanyar amfani da wasu ƙananan robobi, ga kuma yadda aka samar da sauyi wajen yadda ake yi wa yara kaciya, kuma cikin ikon Allah ta warke a kwanaki kaɗan, saboda irin magungunan tsayar da jini da muke amfani da su. Duk waɗannan abubuwa da muke yi muna yi ne tare da wasu yara matasa da muke koyawa wannan sana’a, don su ma su taso su cigaba da raya ta, kuma ta zama musu hanyar cin abinci.

Game da batun matasa da ka yi, anya kana ganin matasan mu na da sha’awar irin waɗannan sana’o’i na gargajiya?

E, babu shakka sana’o’in mu na gargajiya na fuskantar koma baya, saboda rashin shigar matasa sosai da za su iya kawo sauye-sauyen zamani a cikin su. Sai dai mu a ɓangaren wanzamai muna ƙoƙarin shigar da yaran mu da na maƙwafta da sauran jama’a da ke nuna sha’awar shiga wannan sana’a, sakamakon halin da ake ciki na matsalar rashin aikin yi da tsadar rayuwa.

Waɗanne hanyoyi ne ka ke ganin gwamnati da hukumomi za su shigo don su taimaka wajen inganta wannan sana’a taku?

Lallai akwai buƙatarsa hannun gwamnati cikin ƙoƙarin samar wa irin waɗannan sana’o’i namu na cigaba da bunƙasa. Kamar wannan sana’a tamu wacce tsohuwar sana’a ce ta tun farkon tarihin ɗan Adam, wacce ta kasance jigo wajen abin da ya shafi kiwon lafiyar al’umma.

Idan ka tuna wanzami shi ne likitan al’umma, shi ne mai ba da magani, shi ne likitan ido, likitan haƙori da sauran cututtuka. Amma bayan zuwan turawa sai aka yi watsi da wannan sana’a, saboda fitowar tsarin asibiti, sai ana yi wa sana’ar tamu kallon wani abu na koma baya. Alhalin a baya da wanzaman ake taƙama, wajen maganin cututtuka.

Yaya aka yi ka samu kan ka a matsayin Sarkin Askan Jihar Filato?

Alhamdulillahi. Ka san shi shugabanci na Allah ne, kuma shi ne ke ba da shi ga wanda ya so. Bisa tsari na wannan masarauta da yadda tsarin shugabanci ya ke na gargajiya ana ba da sarautar Sarkin Aska ne ga wanda ya gada daga iyaye da kakanni. Ni ma hakan ce ta faru, kakana ne ya fara kafa wannan masarauta a nan Jos, tun zamanin Turawan mulkin mallaka, a shekarar 1910 kamar yadda muka samu a rubuce-rubuce na tarihi.

Haka kuma wannan tsari ya yi ta tafiya har ya kawo kan mu. Nima kuma na gaji wannan sarauta ne daga mahaifina, bayan da Allah ya yi masa rasuwa a shekarar 2010, lokacin shekaruna ba su wuce 40 ba.

Yaya ka ke haɗa hidimar tafiyar da harkokin masarauta da sauran ƙungiyoyin da ka ambata a baya?

To, ai ita masarauta kamar matsayin uwa ce, a wannan sana’a, sauran ƙungiyoyi suna tafiya bisa umarni da shawarwarin masarauta. Akwai matasa da muke da su wayayyu waɗanda suka samu ilimin rayuwa, su ne muke wakiltawa suke tafiyar da harkokin ƙungiya domin yadda zamani ya ke tafiya.

Hukumomi da gwamnati ba za ta yi magana da ku kai tsaye ba, sai ta ƙarƙashin ƙungiya mai rijista. Muna da dukkan tsare-tsaren da ake buƙata na ayyukan ƙungiya, kuma muna ba da gudunmawa a duk inda buqatar hakan ta taso.

Yaya alaƙar wannan masarauta da gwamnati da kuma jagorancin da ake da shi na sarautun gargajiya a Jihar Filato?

Babu shakka muna da kyakkyawar alaƙa da su. Domin ai tun a tarihi ma kowacce fada a Arewa tana da malaminta, wanda shi ne limamin gari, da kuma likitan fada wanda shi ne Sarkin Askan garin, kuma shi ma saraki ne da ke da mabiya a bayansa waɗanda su ma ana yi musu naɗi na rawani a matsayin su na ’yan faɗar Sarkin Aska.

Wannan masarauta tamu tana da gurbi na musamman a fadar shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Filato, wato Mai Girma Gbong Gwom Jos, kuma tana biyayya ga faɗar shugaban Sarakunan Gargajiya na Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa wato Ujah na Anaguta. Muna zuwa mu yi gaisuwa, kuma muna halartar tarukan su don ƙarfafa sarautun gargajiya da raya al’adunmu.

Tun da ka hau kan wannan kujera, waɗanne sauye-sauye za ka iya cewa an samu a ƙarƙashin jagorancinka?

Alhamdulillahi. Daga lokacin da na hau kan wannan kujera bisa ƙaddarawar Ubangiji, shekaru goma sha biyu kenan, na samu nasarar samar da canje-canje, tare da sauran abokan aiki da muke wannan hidima tare. An samu ƙarin haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin wanzaman Jihar Filato baki ɗaya, da kuma haɗe kan kungiyoyin wanzamai daga dukkan ƙananan hukumomin Jihar Filato, ƙarƙashin jagoranci ɗaya.

Mun samu nasarar farfaɗo da masarautun da a baya suka fara mutuwa, idan mai riƙe da sarauta ya rasu sai a rasa mai gadon sa a gidan to, mun yi ƙoƙarin ƙarfafa gwiwar wasu daga cikin iyalan irin waɗannan magabata namu, don su dawo su rungumi gadon gidan su. Kuma mun yi nasara a kan da dama daga cikinsu.

Sannan har wa yau mun yi ƙoƙarin ganin an samu kafuwar ƙungiyoyin matasa wanzamai don ƙara jawo sauran matasa masu tasowa a jiki. Mun kuma samu nasarar isa ga sauran ‘yan uwan mu wanzamai na wasu jihohin Arewa, inda muke da alaƙa mai ƙarfi da kyakkyawan zumunci a tsakanin mu da su. Alhamdulillahi.

Akwai wani ƙalubale da ka ke so a ce a lokacin ka an samu nasarar kawar da shi?

Babban ƙalubalen mu shi ne irin yadda gwamnati ba ta kallon irin waɗannan sana’o’i da martaba, domin su ma su ba da nasu irin gudunmawa, musamman mu a nan Jihar Filato. A wasu jihohin Nijeriya muna ganin yadda gwamnatocinsu ke jan su a jiki, da shigar da su cikin wasu harkoki na moriya, yadda za su amfana kuma su tallafi sana’ar su. Kamar misali a Jihar Katsina, Gwamna Ibrahim Masari, ya ɗauki shugaban ƙungiyar wanzamai Farfesa Bashiru Aliyu Sallau, inda ya ba shi Shugabancin Hukumar Raya Al’adu ta Jihar Katsina.

Sannan duk shekara gwamnatin jihar ta kan ɓullo da tsarin tafiya da wanzaman jihar zuwa aikin Hajji, don yi wa mahajjatan jihar aski, inda ake shigar da su cikin kwamitoci da ba su kujerun Hajji. Mu ma kuma a nan muna ta ƙoƙarin ganin an samu irin wannan damar, amma har yanzu abin ya gagara. Sannan za ka ga a wasu jihohin ana shigar da wanzamai cikin harkokin kiwon lafiya, musamman a ƙananan asibitoci na karkara, mafi kusa da al’umma, domin kula da wasu al’amura da suka shafi inganta lafiya.

Yaya ka ke hangen wannan harka ta wanzanci nan da wasu shekaru masu zuwa?

Insha Allah, muna da kyakkyawan fatan nan gaba, harkar wanzanci za ta bunƙasa sosai, za a sake samun dabarun zamanantar da harkar da shigo da sabbin dabaru. Duba da yadda manyan ƙasashe irin China ke cigaba da inganta harkokin wanzancinsu na gargajiya zuwa fasahar zamani. Mu ma in sha Allahu wata rana za mu kai ga haka, idan aka samu tallafin da ya dace.

Wacce karin magana ce ta ke tasiri a rayuwarka da harkokin ka na sana’a?

Kowa Ya Bar Gida, Gida Ya Bar Shi!

Na gode.

Nima na gode sosai.