Muna zaman lafiya da sauran ƙabilun garin Legas, inji Wazirin Obalande

Daga DAUDA USMAN USMAN a Legas

An bayyana cewa a halin yanzu al’ummar Hausawa mazauna garin Legas ba suda wata matsala a tsakanin su da sauran ƙabilu mazauna Jihar Legas.

Hakan ya fito ne daga bakin Wazirin Marigayi Malam Adamu, Sarkin al’ummar Hausawan Obalande da ke Legas, Alhaji Salisu Mohammed Malam Madori, jim kaɗan bayan buɗe bakin azumi a ƙarshen makon nan.

Malam Madori ya ƙara da ce, “haƙiƙa an samu kyakkyawar zamantakewa tsakanin sauran ƙabilu da Hausawa mazauna garin Legas, inda muke ƙara samun fahimtar juna, wanda har auratayya ana yi a tsakani a yankin Obalande.”

Ya yi addu’a da fatan Allah Ubangij ya ƙara ba dawwamar da zaman lafiyar da ke tsakanin su da kuma sauran ƙabilu mazauna garin Legas. 

Ya kuma hori dukkan ƙabilu da su cigaba da haɗa kawunan su don samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Hakazalika, ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su ji tsoron Allah su kuma saka tausayin marasa ƙarfi a zukatan a wannan wata mai alfarma, wajen yin rangwame a kayayyakin masarufi maimakon tsawwalawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *