Musabaƙa: Ganduje ya gwangwanje Gwarzo da Gwarzuwa da kyautar milyan N5

Daga UMAR M. GOMBE

An kammala Musabaƙar Karatun Ƙur’ani ta Ƙasa karo na 35 a Kano tare da Muhammad Auwal Gusau daga jihar Zamfara a matsayin wanda ya zama gwarzo a ɓangare maza, yayin da Nusaiba Shu’aibu Ahmed daga Kano, ta zama gwarzuwa a ɓangaren mata.

Albarkacin bajintar da suka nuna a yayin gasar ya sa Gwamnatin Kano ta yi wa jaruman biyu kyautar kuɗi ta Naira milyan N2.5 ga kowannensu.

Da yake jawabi a wajen rufe gasar Asabar da ta gabata, Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, a bisa wakilicin mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce maza 180 da mata 190 daga daga jihohin ƙasar nan 36 haɗa da Birnin Tarayya, Abuja, suka fafata a gasar wadda ta gudana na tsawon kwanaki 9 a harabar Jami’ar Bayero da ke Kano.

Ganduje ya ce ya lura da yadda jaruman suka fafata a duka rukunai guda shida na gasar, tun daga kan izifi 2 da Tajwid har zuwa izifi 60 da Tafsiri.

Ya ci gaba da cewa gwamnatinsu ta bai wa fannin ilimin Islamiyya muhimmanci musamman ma karatun Alƙur’ani da kuma haddace shi a dukkanin matakai.

Ya ce, “Wannan ne ma ya sa muka ƙirƙiro Hukumar Kula da Makarantun Islamiyya ta Jiha wadda irin ta kenan ta farko da aka taɓa samu a jihar.”

Ya bada tabbacin ci gaba da tallafa wa sha’anin gasar karatun Alƙur’ani a duk lokacin da aka yi nufin gudanar da ita.

A nasa ɓangaren, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Nijeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce gasar karatun Alkur’ani wadda aka saba shiryawa domin fito da alfanun karatun na ci gaba da samun tagomashi duk shekara.