Musawa za ta iya fuskantar ɗauri saboda karya dokar liƙi da Naira

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An samu sabon Ministar Fasaha, Al’adu, da Tattalin Arziki tana liƙi da kuɗin Naira.

Musawa tana cikin wasu ministoci 44 da aka rantsar a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, 2023, don zama mambobin majalisar ministocin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Da yammacin ranar ƙaddamar da bikin, wani hoton bidiyo ya nuna Musawa tana watsawa wata mawaƙiya takardar Naira a wani taron murnar nasarar da ta samu na zama minista.

Dokar ta ci karo da sashe na 21 na dokar babban bankin Nijeriya (CBN) na shekarar 2007.

Dokar ta CBN ta bayyana cewa yin ta’ammali na liqi da Naira zai janyo zaman gidan yari.

A cewar dokar, duk wanda aka kama da aikata laifin yana da laifi, kuma yana iya fuskantar ɗaurin watanni shida a gidan yari ko kuma za a ci shi tarar Naira 50,000 ko kuma a ci shi tara da kuma ɗauri.

Babban bankin na CBN ya bayyana a cikin dokar cewa liƙi da Naira cin zarafi ga kuɗin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *