Daga CMG Hausa
Musulmai a jihar Xinjiang ta ƙasar Sin, sun gudanar da shagulgula daban daban na bikin ƙaramar Sallah a jiya Laraba.
Wasu musulmai a birnin Urumqi, sun gudanar da sallar idi ne a masallacin Yangxing mai tarihin sama da shekaru 120, ƙarƙashin matakan kariya da daƙile yaɗuwar annobar COVID-19. A harabar masallacin Etigar dake Kashigar kuwa, mazauna na ƙabilu daban-daban ne suka yi kwalliya tare da gudanar da shagulgulan bikin ranar Sallar.
Ranar Sallah, rana ce da iyalai a jihar Xinjiang ke ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki, inda suke haɗuwa su yi ciye-ciyen nau’ikan abinci don murnar bikin.
Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa