Mutane 1,040 ne suka amfana da tallafin kayan abinci da mawaƙi Rarara ya yi a Katsina

Daga AISHA ASAS

Shahararren mawaƙin siyasa, kuma babban mawaƙin Jam’iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara, ya bayar da tallafin kayan abinci ga mabuƙata, a ƙoƙarin ganin ya bayar da tasa gudunmawa a samun sasaucin matsin rayuwa da ake ciki.

Mawaqin ya bayar da wannan tallafi ne a mahaifarsa, Kahutu da ke Ƙaramar Hukumar Danja, ta Jihar Katsina, kamar yadda babban mai taimaka wa mawaqin a kafafen sada zumunta Rabi’u Garba Gaya ya bayyana.

Rabi’u ya ce, Rarara ya gudanar da rabon kayan ne a mahaifarsa da ke Kahutu, sannan an bai wa kowanne mutum ɗaya daga cikin mutanen 1,040 ƙaramin buhun masara, kuma mawaƙin ne da kansa ya jagoranci rabon wannan abincin, wanda hakan zai tabbatar da an yi rabon yadda ya kamata.

Bai tsaya a nan ba, Rabi’u Garba Gaya, ya qara da cewa, bayan buhun masaran, Rarara ya lalewa kowanne daga cikin mutanen da suka samu wannan tallafin Naira dubu uku don ƙarin samun sauqi wurin sarrafa abincin, wato dai kuɗin cefane.

Daga ƙarshe Gaya ya tabbatar da ba a zaɓo mutanen da aka ba wa tallafin na masara da kuma kuɗi bisa son rai ko duba da jam’iyya ba, sai dai duba da wa ya fi buƙata.

“An zaɓo mutanen da ake ganin sun fi dacewa a ba wa tallafin ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ko ra’ayi ba, domin mafi yawa daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin tsofaffi ne da kuma matan da mazajensu suka rasu,” inji shi.

Idan muka yi duba da yanayin da ake ciki yanzu, za mu iya cewa, tallafin mawaqin Dauda Kahutu Rarara ya zo a daidai lokacin da aka fi buƙatar sa, duba da matsayin rayuwa da ke ƙara ta’azzara ga ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *