Mutane 25 sun mutu, 53 sun jikkata a haɗarin mota a Kano – FRSC

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Hukumar kiyaye haddura ta ƙasa FRSC reshen jihar Kano ta tabbatar da mutuwar matafiya 25, yayin da wasu 53 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a safiyar yau Litinin.

Lamarin ya faru ne a kasuwar duniya ta Dangwairo da ke wajen birnin Kano.

An ce matafiyan sun yo lodin su ne a cikin wata tirela wadda ita ma take dauke da shanu ta nufi Kudancin Nijeriya daga Maiduguri.

Sai dai Tirelar ta yi karo da wata motar kuma ta yi ta’adi so sai inda mutane da dama suka mutu.

Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar, Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Litinin a Kano.

Ya ce hadarin ya rutsa da wata tirela (IVECO) mai lamba XA 311 ZB.

“Mun samu kiran gaggawa da misalin karfe 03:15 na safiyar ranar 1 ga watan Yuli, 2024. Da samun labarin, mun aika da jami’an mu da motar mu cikin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru domin ceto wadanda abin ya shafa da karfe 03:30 na safe,” in ji Ibrahim.

Kwamandan sashin ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon wuce gona da iri wajen tukin mota mai hatsari wanda hakan ya janyo rasa natsuwa.

Ya kuma bayyana cewa a yayin aikin ceto kayayyakin da aka kwato sun hada da babura shida, wayoyin hannu guda goma, dabbobi (awaki da raguna), Masara da kudi N400,000.

Abdullahi ya ce duk kayayyakin da aka samu a wajen hatsarin suna hannun ‘yan sanda.

“Ba tare da bata lokaci ba aka kai dukkan wadanda abin ya shafa zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammed Kano domin samun kulawar gaggawa.

“Likitocin da ke bakin aiki sun tabbatar da mutuwar mutane 25 daga cikin wadanda abin ya shafa,” in ji shi.

Ya gargadi masu ababen hawa kan rashin tsaro na safarar dabbobi, kayayyaki, tare da mutane