Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da samun sabbin mutane 28 da aka tabbatar sun kamu da cutar zazzaɓin Lassa tare da rasuwar mutane uku. Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton mako na 10 daga 3 zuwa 9 ga Maris, 2025.
Rahoton ya nuna cewa adadin sabbin waɗanda suka kamu da cutar ya ragu daga 29 a makon da ya gabata zuwa 28 a wannan makon.
Jihohin da abin ya shafa sun hada da Ondo, Bauchi, Edo, Taraba, Kogi, Filato, Delta, da Anambra.
Jimillar masu cutar a shekarar 2025 ya kai 563 tare da mutuwar mutane 103, inda kaso na mace-mace ya kasance 18.3%, wanda ya ragu idan aka kwatanta da shekarar 2024 da ya kai 18.9%.
Jihohin Ondo, Bauchi da Edo sun ɗauki kaso 73% na dukkannin waɗanda suka kamu, inda Ondo ke da 31%, Bauchi 25%, da Edo 17%.
Hukumar NCDC ta bayyana cewa an kafa kwamiti na musamman da ke ɗauke da masu ruwa da tsaki daga ɓangarori daban-daban don yaƙar cutar a matakai daban-daban. Alamomin cutar sun haɗa da zazzaɓi, ciwon kai, ciwon maƙogwaro, gajiya, tari, amai, gudawa, ciwon jiki, da ciwon kirji. A matsanancin yanayi, cutar na haifar da zubar jini daga kunne, ido, hanci, baki da sauran ɓangarorin jiki.